Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na magance matsalar rashin tsaro da ta addabi Kasar ta hanyar bakin haure ba bisa ka’ida ba a kan iyakokin Nijeriya.
Mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar harkokin cikin gida Mista Afonja Ajibola ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da yafitar a ranar Laraba a Abuja.
A cewarsa, babban sakataren ma’aikatar, Dr. Shuaib Belgore ne ya bayyana hakan a Legas yayin da yake gabatar da jawabi a karo na 3 na koyar da harkokin tsaro na kasa da kasa da ya gudana a cibiyar kula da harkokin kasa da kasa ta Nijeriya NIIA.
Belgore ya ce ma’aikatar ta hannun hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya (NIS) ta bullo da sabbin hanyoyin inganta harkokin kula da sanya Ido kan iyakoki.
Sakataren, ya kara da cewa irin wadannan sabbin abubuwa za su taimaka wajen tunkarar kalubalen da ke tasowa a karni na 21 da ke ci gaba da yin barazana ga tsaron cikin gida na Nijeriya.