Jihohi uku, da suka hada da Ebonyi, Gombe da kuma Nasarawa sun mika bukatar gwamnatin tarayya ta karbi harkokin gudanar da filayen jiragen saman jihohin su, bukatar da gwamnati ta amince da ita. Wannan kuma yana nufin cewa, a ‘yan kwanaki masu zuwa dole gwamnatin tarayya ta amayo wasu biliyoyin nairori don mayar wa da gwamnatocin wadannan jihohin, misali a nan shi ne gwamnatin Jihar Nasarawa ta mika bukatar Naira Biliyan 10 ga gwamnatin tarayya na karbar ragamar filin jiragen sama dana daukar manya kaya na garin Lafia da ke Jihar Nasarawar.
Babban abin da ya kamata a fahimta a nan shi ne wadannanfilayen jiragen sama da aka gina a jihohin nan uku duk an yi sune da manufar siyasa kawai ba wai don wani buri na bunkasar tattalin arziki ba.
- Tsare-tsaren CBN Don Samar Da Kyakkyawar Alkibla Ga Tattalin Arzikin Nijeriya
- Mutane 8 Sun Mutu, 2 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kogi
Muna wannan bayanin ne don tunda farko akwai filayen jiragen sama da al’ummar wadannan jihohin za su iya amfani da su ba tare da wata matsala ba, misali, jihar Ebonyi za ta iya a cikin sauki da filin jiragen sama na garin Inugu; Jihar Gombe za ta iya amfani da na garin Bauchi yayin da filin jirgin sama na jihar Benuwai zai iya zama abin amfani ga al’umma JIhar Nasarawa.
Duk da cewa, ana sa ran filayen jiragen saman su samar da kudin shiga amma bincikenmu ya nuna cewa, cikin filayen jiragen sama 22 da muke da su a Nijeriya filayen jirgin sama na Legas, Fatakwal, Kano da kuma Abuja ne kawai kuma wadanda dukkansu hukumar Kula da filayen jiragen saman ta Nijeriya ke kula da su kadai ke samar da kudin shigar da za a iya magana a kai.
A ra’ayin wannan jaridar, shawarar wasu gwamnonin jihohi ta samar da filayen jiragen sama abu ne da ba zai haifar da da mai ido ba. Yawanci su suna gina filayen ne don cimma wani buri na kashin kansu. Wanann kuma abin takaici ne in har muka lura da cewa, gina filin Jirgin sama abu ne da yake bukatar dinbin kudade masu yawan gaske.
Mai zai sa jihar da take rarrafe tare da neman kudaden gudanar da ayyukanta za ta fara kaddamar da gina filin Jirgin sama tun da farko? Wannan kamar an yi ne kawai don biyan bukatar wasu kalilan daga cikin al’ummar jihar masu hannun da shuni, maimakon a karkatar da kudaden wajen samar da hanyoyin warware matsalolin da al’umma ke fuskanta na rashin Ruwan sha da hanyoyi da wutar lanytar da sauran ababen more rayuwa da mafi yawan mutanen jihohin ke fuskanta.
A bayyana yake cewa, gwamnatin Jihar Ebonyi ta yanzu da gwamnatocin da suka shude a jihohin Gombe da Nasarawa ba su yi bincike na yadda kamata ba kafin su tsiri fara gina filayen jirgin sama a yankunan nasu, da gwamnatocin wadannan jihohin sun yi wannan bincike da basu kai yin haka ba don yin wannan aikin tamkar rashin sanin abin da ya kamata a muhimmantar da shi ne a rayuwar al’umma gaba daya.
Idan za a yi adalci ga GwamnaAbdullahi Sule da Gwamna Muhammadu Yahaya, wadanda suka gada Tsofaffin gwamnonin jihohin da suka hada da Umaru Tanko Al-Makura da Danjuma Goje sune suka kirkiri gina filayen jiragen saman a jihohin Nasarawa da Gombe.
Ana iya cewa, ba zai yiwu Gwamna Sule da Gwamna Yahaya, wadanda dukkan su ‘yan kasuwa ne su rungumi irin wannan harkar ta samar da filayen sama tun da farko ba.
Amma ga Gwamnan jihar Ebonyi, Dabe Umahi wannan kamar wani babbar rashinm muhimmantar da abin da al’umma ke bukata ne. Ba tare da la’akari da yadda jihar za ta fuskanci kula da filin jirgin sama ba kawai sai ya fada gina filin jirgin sama na kasa da kasa, sai kuma ga shi wai yana neman gwamnatin tarayya da ta karbi ragamar gudanar da filin jirgin, wanda ya gada tsohon gwamna Dakta Sam Egwu ya yi irin wannan kuskuren inda ya gina katafariyar cibiyar masana’antu a garin Abakaliki wadda al’umma suka rasa cikakken amfaninta.
Idan za a iya tunawa a shekarar da ta gabata ne Gwamna Umahi ya rubuta wa gwamnatin tarayya bukatar neman bashin Naira Biliyan 10 don sayen kayayyakin aiki na filin jirgin sama, yana mai cewa, da zarar an kamala aikin za su mika filin jirgin ne ga gwamnatin tarayya.
Kwanaki ne kuma Gwamna Umahi ya sanar da gina gidan gwamnatin jihar a kan kudi Naira Biliyan 1.2 a garin Abuja wannan ma wani aikin baban giwa ne.
Ra’ayin wannan jaridar shi ne, in har gwamnatin tarayya ta kuskura ta karbi ragamar wadannan filayen jiragen saman to kamar ta ba wasu jihohi damar shiga sahun irin wadannan aikin ne na baban giwa da ba zai yi wa al’umma amfanin komai ba.