In mun ambaci manyan kwazazzabai 3 na kogin Yangtze, wato Sanxia na koginYangtse, tabbas ne kun san shi sosai, domin ya fi kyan gani da ban mamaki a duk kogin Yangtze.
Yana da asalinsa ne daga gundumar Fengjie ta birnin Chongqing dakekudu maso yammacin kasar Sin, sa’an nan karshensa yana cikin birnin Yichang nalardin Hubei. Ya yi suna matuka ta fuskar yawon shakatawa a kasar Sin.
- Sojoji Sun Kubutar Da Dalibar Chibok Tare Da Tagwaye ‘Yan Watanni 4
- An Sake Yin Juyin Mulki A Burkina Faso Bayan Wata 8
A halinyanzu, a yankin yawon shakatawa na Sanxia, gine-ginen madatsar ruwa na Sanxiasun fi jawo hankali.
Tsawon manyan kwazazzabai 3 na kogin Yangtze, ko kuma Sanxia na koginYangtze, gaba daya ya kai kilomita 193, wadanda suka hada da kwazazzabanQutangxia, da Wuxia da kuma Xilingxia.
An gina katuwar madatsar ruwa ta Sanxia abangaren tsakiya na kwazazzabon Xilingxia, wadda take daya daga cikin gine-ginenyin amfani da ruwa mafiya girma a duk duniya.
An fara gina madatsar ruwa ta Sanxia daga shekarar 1994, wadda take taka muhimmiyar rawa a fannonin daidaita ambaliyar ruwa, da samar da wutar lantarki, da zirga-zirgar jiragen ruwa, da yin amfani da ruwa yadda ya kamata.
Haka kuma,wannan katuwar madatsar ruwa, ginshiki ne na tashar samar da wuta ta hanyar amfanida ruwa ta Sanxia.
Mutane masu dimbin yawa daga gida da wajen kasar Sin, suna ziyartar gine-ginen madatsar ruwa ta Sanxia a kowace shekara, domin kara saninsu kan yadda ake amfanida ruwa, da ni’imtattun wurare da wuraren yawon shakatawa ta fuskar al’adu.
Liao Mengxing, mai jagorantar masu ziyara a wurin yawon shakatawa na manyankwazazzabai 3 na kogin Yangtze, ya yi karin bayani da cewa, “Yau mun tashi dagabirnin Yichang, ta hanyar mota ta musamman, mun shiga yankin madatsar ruwa,muna bukatar canza motarmu a cibiyar masu ziyara.
Maziyarta ba za su iya fara ziyaraa yankin yawon shakatawa na Sanxia ba, sai sun canzan motarsu, kuma an yi musubincike a tsanake.
Su kan fara ziyartar ayyukan madatsar ruwa na Sanxia daga tudunTanziling.”
Yankin yawon shakatawa na ayyukan madatsar ruwa na Sanxia, ya bude kofarsassansa 3 kawai ga masu ziyara, wato tudun Tangziling, da dandalin Yibawu, dalambun tunawa da katse ruwa a kogin Yangtse.
Da farko mun isa tudun Tanziling,wuri ne mafi tsayi a wannan yankin yawon shakatawa. Tsayin tudun ya wuce mita 260daga leburin teku. In an tsaya a wajen, ana iya hangen duk yankin yawon shakatawar.
A game da asalin sunan tudun Tanziling, akwai wata almara. Liao Mengxing ya yikarin bayani da cewa, an ce, a can da, Da Yu wanda ya kafa zamanin daular Xia, yadukufa wajen jagorancin jama’a a yaki da ambaliyar ruwa, wadda ta addabi al’ummamatuka, har bai koma gida ba cikin dogon lokaci.
A sakamakon taimako daga wani Samai tsarki, an haka hanyar ruwa mai tsawon mita 200, wato Sanxia na kogin Yangtse.
Wadanda ke zaune a wurin sun yi masa godiya matuka, ta haka suka shirya ba waDa Yu kyautar giya ta babbar kwalaba guda, sun tuka wani katon jirgin ruwa domindaukar kwalabar.
Amma Da Yu ya riga ya tafi tare da shanun, ya bar wani katon dutseda ya zama abun tunawa. Hakan ya burge mazauna wurin sosai, har ma ba su sonkomawa gida, sun yi ta jira a kogin.
A kwana a tashi, a karshe dai katon jirgin ruwanya zama wani karamin tsibiri, wato tsibirin Zhongbaodao, inda aka kafa madatsarruwa ta Sanxia.
An ajiye kwalabar mai cike da giya mai dandano a gabar hagu takogin, sannu a hankali kwalabar ta zama tudun Tanziling. An ce, in ana rana sosai,kuma akwai dan iska, ana iya jin kamshin giya.
Idan an hangi duk ayyukan madatsar ruwa na Sanxia daga tudun Tanziling, ana iya isa dandalin Yibawu.
Dalilin da ya sa aka kira wannan dandali da sunan Yibawu,wato dari 1 da tamanin da biyar shi ne, tsayin dandalin ya yi daidai da na madatsarruwa ta Sanxia, wato mita 185 daga leburin teku. Liao Mengxing ya ce, a yayin daake tsayawa a dandalin Yibawu, ana iya fuskantar madatsar ruwa ta Sanxia, tare da jindadin kallon kyan surar kogin Yangtze.
Ana iya more ido da madatsar ruwa ta Sanxiaba tare da daga kai ba, kuma ana iya hangen shahararriyar gundumar Zigui, wandagari ne na marigayi Qu Yuan, mashahurin marubucin rubutattun wakoki na zamanin da.
Ayyukan madatsar ruwa da suka fi girma a duk duniya ta fuskar amfani da ruwa,dake tsaye a kwari a mike, sun girgiza mutane sosai.
Mista Sun da ya fito daga birninWuhan da ke yankin tsakiyar kasar Sin, a karo na farko ya ziyarci ayyukan, abin daya shiga zuciyarsa matuka.
Sun ya bayyana cewa, a karo na farko, ya ziyarci madatsarruwa ta Sanxia. Ya duka kai daga tudun Tanziling, Ayyukan madatsar ruwa na Sanxiamai girma sun bayyana a gabansa, sa’an nan a yayin da ya isa dandalin Yibawu, ya kara fahimtar kyan surar madatsar ruwan a kurkusa. Ayyukan madatsar ruwa na Sanxia su ne ayyuka zalla mafi girma da ‘yan Adam suka gina domin amfani da ruwa.
Bayan masu yawon shakatawa sun sauka daga dandalin Yibawu, su kan yi shirin zuwa wurin shan iska na tunawa da katse ruwa a kogin Yangtse, wanda wurin shaniska ne na farko da kasar Sin ya gina ta fuskar ayyukan amfani da ruwa.
Wannanwurin shan iska na dogara da babban tsauni, yana kuma fuskantar madatsar ruwa.Liao Mengxing ya bayyana cewa, ana iya kara ilmin yadda aka kaddamar da ayyukanmadatsar ruwa na Sanxia a wannan wurin shan iska, inda ya ce, wurin shan iska natunawa da katse ruwa a kogin Yangtse, yana bangare na kasa a gabar kogin Yangtsea kudu.
Fadinsa ya fi girma a duk yankin yawon shakatawa na ayyukan madatsarruwa na Sanxia.
Hakika wannan wuri ya fi dacewa da jin dadin kallon ayyukan. Anaiya kara sanin manyan injunan da aka taba amfani da su, a yayin da ake gudanar da ayyukan, kamar kattan motoci da kuma wurin tarihi da aka kaddamar da ayyukan.
Ayyukan madatsar ruwa na Sanxia, babban burin al’ummar Sin ne wanda sukadauki shekaru 100 suna kokarin cimmawa. Ayyukan madatsar ruwan na kiyaye mutane kimanin miliyan 15 a sararin kasan Jianghan da yankin kogin Dongtinghu, dagonaki masu fadin eka miliyan 1 da dubu 530.
Sun taka muhimmiyar rawa a fannoninkandagarkin abkuwar ambaliyar ruwa, da samar da wutar lantarki, da zirga-zirgarjiragen ruwa.
Hakika dai, tun lokacin da aka fara gina madatsar ruwa ta Sanxia a shekarar 1995,masu ziyara da yawa sun fara yin ziyara, sabili da kammala ginawa, da kuma faraamfani da madatsar ruwan, masu ziyara na gida da wajen kasar Sin sun kara zuwa wajen.
Duk da haka, Hu Nianyao, jami’in kula da yankin yawon shakatawa na Sanxia nakogin Yangste yana ganin cewa, kamata ya yi a habaka fannonin yawon shakatawa a Sanxia na kogin Yangtse, a maimakon zazzagayawa kawai.
Hu ya ce, ba mu bunkasaaikin yawon shakatawa sosai ba. Nufinmu shi ne kokarin sabunta hanyar yawon shakatawarmu, amma ba tare da gurbata muhallin halittu ba, a maimakon kara wamutane ilmi ta fuskar kimiyya da fasaha kawai.
Hu Nianyao ya yi karin bayani da cewa, a yankin madatsar ruwa ta Sanxia, za ayayata tunanin kiyaye muhallin halittu.
Alal misali, za a dakatar da yin amfani daabubuwan da ba a iya sake amfani da su. Dalilin da ya sa masu yawon shakatawa sukeziyarci yankin shi ne, bude ido da sakin jiki, don haka yin bayani kawai ba zai gamsarba. Ya zama tilas a sabunta hanyar yawon shakatawa.
Hu ya ce, baya ga abubuwan da ake iya gani, muna kokarin sanya masu ziyara suiya kara fahimtar karin abubuwa da kansu kai tsaye.
Alal misali, katse ruwan koginYangtze, lamari ne da ka iya girgiza mutane matuka. Shin za mu iya samar wa masuziyara wata damar kara fahimtar lamarin ta hanyar shiga ciki? Ban da wannan kuma, ana amfani da fasahohi iri iri guda 4, a ayyukan madatsar ruwa na Sanxia, wadandaaka ba su lambobin yabo na gwamnati ta fuskar ci gaban kimiyya da fasaha, munakokarin bayyana yadda muke amfani da wadannan fasahohi, ta yadda za su iya karailmin yadda Sinawa ke daidaita matsalar ambaliyar ruwa.
Ma iya cewa, bayan da madatsar ruwan ta fara samar da wutar lantarki ta hanyaramfani da ruwa, Sanxia na kogin Yangtze, ya kara kyan gani.
(Mai fassarawa: TasallahYuan daga CMG Hausa)