Ranar 5 ga watan Oktoban kowace shekara, ita ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don bikin murnar ranar Malamai ta Duniya.
A yau malamai da dama a sassan duniya na murnar zagayowar wannan rana, amma a Nijeriya abun ba yabo ba fallasa.
- Gwamnatin Jihar Imo Ta Amince Da Karin Matsayi Da Tallafin Kiwon Lafiya Kyauta Ga Ma’aikatanta
- Zambar Naira Miliyan 55: ICPC Ta Fara Bin Diddigin Dan Kwangilar Dam Din Jihar Filato
Idan aka yi waiwaye musamman ga ilimin da ya shafi Jami’o’i wanda ya hadar da malamai da dalibai, a iya cewa ‘ba a rabu da Bukar ba an haifi Habu.’
ASUU da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya sun shafe kimanin watanni bakwai zuwa takwas suna tafka takaddama kan yajin aikin da ya ki ya ki cinye kan wasu alkawura da malaman Jami’o’in suka tilas ne sai an biya musu.
Idan aka yi waiwaye za a fahimci cewar yajin aikin ASUU abu ne da aka shafe kimanin sama da shekaru 30 ana yinsa, a iya cewa kusan kowace gwamnati ta zo sai an yi wannan takaddama ta yajin aiki.
Wasu gwamnatocin kan yi kokarin ganin sun biya wasu bukatun da ASUU ke nema sannan ta dauki alkawarin cika wasu, wanda a wasu lokutan hakan ke jefa wata gwamnatin cikin kaka-na-kayi idan ta gaji wata gwamnatin.
A shekarar 2012, gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta daukar wa ASUU alkawura wanda gwamnatin yanzu kuma ta gada, hakan ya sa ake ta kwan-gaba-kwan-baya.
Sai dai dag bangarenta, ASUU na ganin kamar gwamnatin yanzu na nuna halin ko in kula game da illar da yajin aikin ka iya haifar wa fagen ilimi.
Sannan ta soki lamirin gwamnatin tarayya kan tsarin biya ma’aikata albashi na IPPIS, wanda ta ce akwai lauje cikin nadi game da tsarin, wanda hakan ya sa tun fil-azal taki karbar tsarin.
Idan aka yi duba kuwa game da koma baya da yajin aikin ya haifar, a iya cewa akwai bukatar kowane bangare ya mayar da wukarsa don cimma matsaya tare da bai wa dalibai da su kan su malamai damar gudanar da ayyukansu yadda ya dace.
Yajin aikin ya kawo koma baya ga dalibai da yawa, musamman daliban da ke shirin kammala karatu da kuma wanda suke jiran a kammala duba kundin bincikensu don ba su takardar shaidar kammala Jami’a.
A bangaren malaman kuwa, su ma suna fama da rashin albashi, wanda hakan ya jefa da dama daga cikinsu cikin mayuwancin hali, musamman abin da ya shafi tafi da harkokin gida na yau da kull da kula da karatun yara.
Gashi gwamnatin tarayya ta kafa dokar duk wanda bai yi aiki ba, ba shi da albashi.
Wannan hali da ake ciki, ya sanya mutane da dama yin kiranye-kiranye ga gwamnatin tarayya da ma bangaren ASUU na ganin kowa ya dauki dangana, don ciyar da ilimi gaba da kuma kyankyasar da matasa masu ilimi da su jagoranci Nijeriya a nan gaba.
Da fatan kowane bangare zai duba na tsanaki, da bai wa zuciyarsa ruwan sanyi don daina tafasa kan wannan yajin aiki da ya ki ci ya ki cinyewa.