Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nemi duk wani ɗan jam’iyyar ya bayar da tasa gudunmawar ta yadda za a haɗa ƙarfi da ƙarfe don ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaɓen 2023 da ke ƙaratowa.
Ya nunar wa mambobin APC cewa dole su kimtsa cikin muddin ana da buƙatar jam’iyyar ta ci gaba da riƙe madafun iko a 2023, yana mai cewa buƙatar jam’iyyar na gagidaba da ta kowane mamba ko ƙungiya.
Adamu ya ce sakamakon taron APC da ya gudana ranar Talata shi zai tantance nasarar da jam’iyyar za ta samu a 2023.
Shugaban jam’iyyar ya bayyana haka ne a wajen Babban Taron APC a Talatar da ta gabata a dandalin Eagle Sƙuare da ke Anuja.
Haka nan, Adamu ya yi gargaɗin cewa dole jam’iyyar ta maganace rikicin cikin gidan da take fama da shi don tabbatar a nasarar jam’iyyarsu a zaɓe mai zuwa.
Ya ce kada a sanya son-kai cikin lamarin neman tsayar da wanda zai yi wa jam’iyya takarar Shugaban ƙasa.
Don haka ya jaddada buƙatar da ke akwai a haɗa kai da fahimtar juna da sassantawa a tsakanin ɗaukacin mambobin jam’iyyar.
A nasa ɓangaren, Shugaban Kwamitin shirya taron kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu, ya ce ‘yan takara 23 ne za su fafata a zaɓen fitar da ɗan takarar.
Ya ƙara da cewa, daliget uku-uku daga kowace ƙaramar hukuma a tsakanin ƙananan hukumomi 774 da ake da su a faɗin ƙasa za a bari su kaɗa ƙuri’a daidai da tanadin Dokar Zaɓe ta 2022 da aka yi wa gyara.
Mahalarta taron sun haɗa da: Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a uwargidansa, Aishat da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan da sauransu.
Har ila yau akwai sauran mambobin jam’iyyar ta APC waɗanda suka yi fitar farin ɗango daga jihohinsu domin halartar babban taron jam’iyyar wanda aka kammala lami lafiya cikin nasara.