Dokta AbdulMalik Atta, daya daga cikin kwamitin shugaban kasa da ya taimaka wajen ceto fasinjojin da aka sace daga jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris, ya zargi mai yin sulhu da ‘yan ta’adda, Malam Tukur Mamu, da kawo cikas ga kokarin sako mutanen da aka sace.
Atta, wanda mahaifinsa na cikin fasinjojin da aka sace, ya yi ikirari ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels.
- Yadda Ta Kaya A Taron Gwamnonin Nijeriya Da Nijer A Katsina
- Dalilinmu Na Yi Wa ASUU Kishiya –Gwamnati
Atta ya ce Mamu ya yi duk abin da zai iya domin dakile yunkurin gwamnatin tarayya na kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su domin amfanin kansa.
Ya ce, “Saboda kawo shawarar amfani da kudi da Mamu ya yi, ya sa iyalan wadanda abin ya shafa sun bayar da dala 200,000 kafin babban hafsan tsaron ya shiga tsakani.
“Kwamitin shugaban kasa ya yi namijin kokari saboda mun shiga dajin mu gana da ‘yan ta’addar har muka da su kwana a daji.
“Yau watanni shida da mako guda kenan, amma mun gode wa Allah komai ya zo karshe a yanzu, sakamakon tallafin da gwamnatin tarayya ta samu ta ofishin babban hafsan sojin kasa. Mun iya shiga daji muka dawo da sauran ‘yan uwa.
“Mun cimma hakan ba ta hannun wani da ya ci amanar kwamitin da gwamnati ba, ina magana ne a kan Tukur Mamu wanda ya dinga dakile kokarin gwamnati don biyan bukatun kansa. Kamar yadda muka sani yanzu yana hannun gwamnati. Amma mun gode Allah, yanzu duk ’yan uwa sun kubuta.
“’Yan ta’addar ba su taba neman kudi a hannun kowa ba, amma Tukur Mamu ya dinga neman kudi a hannun iyalan wanda abun ya shafa ya kuma ya kawo cikas wajen ceto mutanen har na ysawo watanni shida da suka gabata.
“Mun yi asarar kusan Dalar Amurka 200,000. Alhamdulillah hafsan sojin kasa ya dauki nauyin komai da kafa kwamitin da bai taba tambayar kobo ba. Duk wata sadaukarwa da ake yi ya zuwa yanzu ya kasance na kashin kai ne don tabbatar da an sako wadanda abin ya shafa.
“A cikin kwamitin, zan iya tabbatar muku cewa na yi aiki tare da mutane masu dattako. Idan ina da dama, sai na an rabawa kowane lambar yabo. Mun yi kasada da rayukanmu, muka je daji, can muka kwana a cikin daji.
“Mun saurari koken wadancan mutane (’yan ta’adda), duk da mun san abin da suka yi ba daidai ba ne, amma dole mu ja su a jiki.
“Yana da kyau jami’an tsaro su sauya tsare-tsaren ayyukansu kuma ya kamata gwamnati ta kara bude kofa don jan kowa a jiki.”