Jakadiyar Nijeriya a Jamhuriyar Kongo, Deoborah Iliya ta tallafa wa zawarawa da mazajensu suka rasu da marayu da kuma marasa galihu guda 3,000 da kayan abinci da kuma litattafan makaranta a karamar hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna.
A hirarsa da manema labarai jim kadan da kammala bayar da kayan tallafin, jami’inta mai suna Fasto Mathias Sunday wanda ya wakilce ta a wajen rabon kayan ya sanar da cewa, Deoborah ta bayar da talafin ne don ta kara wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar yankin da kuma sauran mutanen jihar tare da kara tabbatar da kauna da dankon zumunci a tsakanin mabiya addinai daban-daban da ke fadin jihar.
Ya kara da cewa, jakadiyar na kuma shirin bullu da shirin horas da marasa galihu koyon sana’o’in hannu domin su dogara da kansu.
Faston ya kuma sanar da cewa jakadiyar ta kafa wani shirin daukar nauyin karatun yara bayan sun zana jarrabawa, inda duk wanda ya samu nasara a jarrabawar za ta dauki nauyin kartun su kyau har tsawo shekaru biyar.
Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba jakadiyar za ta dauki nauyin duba lafiyar wasu daga cikin marasa galihu da ke a jihar kyau.