Abubakar Bakarabe Kofar Na’isa, babban mataimaki na musamman ga Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano, ya ce ‘yan daba da ake zargin mabiya kungiyar Kwankwasiyya ne suka kai masa hari tare da kwace masa wayarsa.
Kofar Na’isa ya yi zargin cewa an daba masa wuka, sannan kuma da yawa daga cikin mutanen da ke wucewa a Kofar Danagundi lamarin ya rutsa da su a yammacin ranar Lahadi.
Bakarabe Kofar Nai’sa, ya bayyana hakan ne a shafin sa na Facebook inda ya bada labarin abin da ya faru.
“Wasu ‘yan daba sun kai min hari yau a Kofar Dan Agundi inda suka daba min wuka suka tafi da wayar salula ta dauke da layin MTN dina.
“Na yi sa’a cikin yardar Allah ban samu wani mummunan rauni ba amma sun yi nasarar kwace wayata.
“Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da kare rayukanmu daga irin wadannan muggan mutane masu mugun nufi,” in ji shi.
Har yanzu kungiyar Kwankwasiyya bata mayar da martani kan wannan zargi ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp