Kamfanin simintin Dangote ya raba wa abokan kasuwancinsa kudi har Naira miliyan 21, ciki har da mutane uku da suka samu kyautar Naira miliyan 5 da aka gudanarwa a Fatakwal.
Mutane uku da suka samu kyautar mega, an sa musu kudaden su ne a asusun ajiyarsu, Naira miliyan 5 kowannensu a wurin taron, yayin da wasu shida kuma suka samu naira miliyan daya kowannen su.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, manajan kasuwanci na yankin shiyyar Kudu-maso-Kudu, David Ademola, ya ce wadanda suka yi nasarar samun kyautar an raba su kashi uku; instant prize, da star prize sai ta karshe super Star prize.
Ya kara da cewa an shirya bada kyaututtukan ne don yaba wa abokan kasuwancin kamfanin masu aminci da mutanen da suka kasance tare da kamfanin (Dangote) tsawon shekaru.
A cewarsa, shugaban kamfanin, Aliko Dangote a kodayaushe yana kan kokarin tallafawa da karfafa abokan kasuwancin mu.
Don haka muna ganin wannan kyauta a matsayin wata hanya ta karfafa wasu daga cikin dillalan mu, abokan cinikinmu a cikin kasuwanci.