Wasu daga cikin maharan da suka kai wa Sanata mai wakiltar mazabar Anambra ta Kudu, Patrick Ifeanyi Ubah, sun shiga hannu.
Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, wanda ya bayyana hakan a wajen bikin birne gawar mahaifin dan majalisa mai wakiltar Njikoka/Anaochal/Dunukofa, Dozie Nwankwo a ranar Juma’a, ya ce wasu daga cikin maharan har yanzu ba su shiga hannu ba amma an yi nasarar cafke wasu.
- Zan Ci Gaba Da Inganta Birane Da Karkara – Gwamna Bala
- Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna A Kauyen Su Jonathan
Ya yi alkawarin cewar ragowar ma za su shiga hannu don fuskantar hukuncin abin da suka aikata.
Idan ba a manta ba Sanata Ubah ya tsalkake rijiya da baya, ba tare da wani abu ya same shi ba inda aka kashe biyu daga cikin jami’an tsaron da fararen hula guda biyu a yayin harin.
Soludo ya jaddada cewar gwamnatinsa na yin kokarin ganin ta kawo karshen ayyukan bata gari duba da cewar ba a san jihar wajen aikata miyagun laifuka ba.
Soludo ya ce: “Sati uku da suka wuce a wannan yankin wasu bata gari suka kai wa Sanata Ifeanyin Ubah hari. Ina so in tabbatar muku da cewar an damke da dama da cikinsu kuma ana gudanar da bincike.
“Ba za mu kyale irin wadannan mutanen su sarara ba. A nan Jihar Anambra, muma zaune lafiya. Dole ne mu rungumi zaman lafiya, duk da zabe na tafe. Anambra tana zaune lafiya.
“Mun yaki bata gari da yawa daga jihar nan. Ba za su kare a dare daya ba, ko a wuraren da aka ci gaba akwai bata gari.”
Soludo ya bayyana jin dadinsa kan yadda ake tafiyar da harkokin siyasa a jihar, a cewarsa duk da bambamcin jam’iyya da ra’ayin ‘yan siyasa hakan bai hana su girmama juna da taimakon juna ba.