Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana fatan jam’iyyarsa ta lashe Jihar Kano da Nujeriya baki daya a zaben 2023.
Tinubu, wanda ya samu gagarumar tarba daga al’ummar jihohin Kano, Jigawa da Zamfara, ya ce abin alfahari ne yadda jam’iyyar APC ke kara karfi a wannan lokaci.
- Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Yi Cikakken Kokarin Shawo Kan Illar Da Ke Tattare Da Yanayin Da Ake Ciki Game Da Rikicin Rasha Da Ukraine
- Bayelsa: Peter Obi Ya Ziyarci Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Bayelsa
Tinubu, wanda ya sauka Kano a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, ya samu tarba daga gwamnonin jihohin Kano, Jigawa da Zamfara, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Alhaji Badaru Abubakar da Alhaji Mohammed Bello Matawalle.
Tun daga filin jirgin saman aka tarbe shi da wake-wake da kade-kade da raye-rayen irin na mutanen jihohin Arewa maso Yamma.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya kai ziyarar kwanaki biyu Kano, inda zai kaddamar da ofishin yakin neman zaben APC a Jihar Kano.
Haka kuma zai kaddamar da wani ofishin Kannywood da ke jihar, sannan daga bisani ’yan kasuwar Kano za su shirya masa liyafar cin abinci.
A cikin shirin ziyarar, Tinubu zai kuma kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, sannan ya gana da sarakunan Gaya da Rano da Bichi da kuma Karaye.
Dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar APC a yayin ziyarar zai gudanar da zaman tattaunawa da kungiyoyin addini daban-daban da suka hada da mabiya darikar Tijjaniyya, Kadriyya, Izalah, shugabannin Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) da kungiyoyin magoya bayan APC na jihar da sauran ayyuka.