• English
  • Business News
Friday, October 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Mahangar ECOWAS Kan Zaben Nijeriya

by Yusuf Shuaibu
3 years ago
ECOWAS

Kungiyar Bunkasa da Tallalin Arzikin Kasahen Yammacin Afirka (ECOWAS), karkashin tawagar kula da shirye-shiryen zabe a Nijeriya ta bayyana mahangarta game da zaben 2023 da za a yi a Nijeriya.

Kamar yadda tawagar kungiyar dai ta bayyana, zaben na 2023 na iya shafar daukacin yankin Yammacin Afirka.Tawagar ta bayyana hakan ne lokacin da ta ziyarci shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu a Abuja a farkon makon nan.

  • Ya Kamata Amurka Ta Soke Takunkumi Idan Tana Son Taimakawa Afirka
  • Ta’addanci Ya Zama Tarihi, Nijeriya Na Cikin Aminci – Lai Muhammad

Tawagardai ta ziyarci shugaban ne a karkashin jagorancin Tsohon Shugaban Hukumar zaben kasar Ghana, Kwadwo Afari-Gyan.

Da yake jawabi a madadin wakilan ,Daraktan Harkokin Siyasa na ECOWAS, Remi Ajiewa ya bayyana cewa yankin yammacin Afirka na neman ganin an samu sahihin zabe a Nijeriya a 2023, domin shugaban Nijeriya yana matukar taka muhimmiyar rawa a yankin.

“Mun san irin muhimmancin Nijeriya a yankin Yammacin Afirka, domin idan Nijeriya ta yi atishawa sai ya shafi daukacin Yammacin Afirka, saboda haka ba ma fatan hakan ya faru.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu

Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba

“Mun zo ne domin mu saurari bayaninka da kuma ganin wuraren da ake samun kalubale domin mu hada rahoto a kai.”

Mista Ajibewa ya kara da cewa sun zo Nijeriya domin hada bincike gabanin zaben 2023 kamar yadda suka saka ido a karkashin ECOWAS a zaben Nijeriyana shekarar 2021.

Ya ce sashe na 11 da 12 da kuma13 na dokokin kungiyar ECOWAS ya tanadi cewa idan za a yi zabe za a hada rahoto ga dukkan mambobin kungiyar, musamman ma zaben shugaban kasa.

“Wannan ne ya sa muka zo Nijeriya wanda muka fara ziyartar shalkwatar ECOWAS tare da tattaunawa da shagabannin kungiyar.

“Bayan nan mun ziyarci ma’aikatan harkokin waje a wannan safiya da sufetan ‘yansanda na kasa da wasu daga cikin kungiyoyin fararen hula da kuma INEC.

“Ko shakka babau, dalilin da ya sa muke gudanar da irin wannan lamarishi ne, INEC kawarmu ce kuma wasu abubuwa da muke ji mukan tattauna domin a samun masalaha.

“Bayan mun tashi daga nan, za mu ziyarci dukkan sassan Nijeriya domin tattaunawa da kwamishinonin zabe. Sannan za mu ziyarci hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya da kuma shugabannin addinai.

“Ba za mu manta da jam’iyyun siyasa ba wajen ganin sun gudanar da ayyukansu kamar yadda tsarin Mulki ya shardanta musu. Haka kuma za mu

gana da kafafen yada labarai kan rawarda suke takawa,” in ji shi.

Mista Ajibewa ya kara da cewa ba wannan ne karon farko da tawagar ta ziyarci Nijeriya ba, domin kuwa sun saba zuwa a duk lokacin da za a gudanar da zabe a kasar ciki har da na 2019.

Da yake jawabi, Shugaban INEC, Farfesa Yakubu ya bayyana cewa hukumarsa ta gayyaci kungiyoyin kasashen duniya domin sa ido a wannan zabe.

Ya kara da cewa wannan ziyarar ta masu sa ido na kasa da kasa tana kara wa hukumar kwarin gwiwa.

“Masu sa ido kan zabe suna da matukar muhimmanci wajen tabbatar da gabin an gudanar da sahihin zabe. A ko da yaushe muna amfanuwa da masu saka ido na kungiyar ECOWAS.

“Alal misali, mun zo ne domin gudanar da bincike, za mu ji daga wurinku irin abubuwan da kuka gano da za su taimaka mana wajen shirye-shiryenzabe.

“Ina bukatar amsar rahotonku wanda za ku kammala a tsakanin watan Fabrairun zuwa Maris, domin mu kara samun ilimi daga ciki,” in ji shi.

Shugaban hukumar INEC ya tabbatar wa tawagar ECOWAS cewaza a yi amfani da na’urorin zamani a zaben Nijeriya na 2023.

Mista Yakubu ya yaba wa tawagar ECOWAS wajen kokarin ganin an gudanar da sahihin zabe a Nijeriya.

Ya ce akwai bukatar ceto dimokuradiyya a dukkan yankunan yammacin Afirka ciki har da kasashen Mali da Burkina da kuma Guinea.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu
Manyan Labarai

Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu

October 24, 2025
Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba
Manyan Labarai

Dauda Lawal Gwarzon Gwamnan 2025: Ceto Zamfara Domin Ci Gaba

October 24, 2025
Buƙatar Daƙile Badaƙalar Amfani Da Takardun Karatun Bogi A Nijeriya
Manyan Labarai

Buƙatar Daƙile Badaƙalar Amfani Da Takardun Karatun Bogi A Nijeriya

October 24, 2025
Next Post
PDP Ta Yi Satar Amsa Daga Manufofin Buhari – Tinubu

Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da Matalauta

Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da Matalauta

October 23, 2025
Shugaban Senegal: Kasar Sin Ta Zama Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Senegal: Kasar Sin Ta Zama Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa

October 23, 2025
Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6, Sun Kama Wasu A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 50, Sun Daƙile Hare-Hare A Borno

October 23, 2025
Me Ake Fatan Gani A Shirin Sin Na Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Na Gaba

Me Ake Fatan Gani A Shirin Sin Na Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Na Gaba

October 23, 2025
Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

October 23, 2025
Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara

Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara

October 23, 2025
Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

Kasar Sin Ta Karyata Rahoto Na Zuki-ta-malle Da Wata Cibiyar Binciken Amurka Ta Fitar Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Yammacin Afirka

October 23, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.