Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na GORON JUMA’A, shafin da ke bawa kowa damar aiko da sakonnin gaishe-gaishensa zuwa ga ‘Yan Uwa da Abokan arziki, na kusa dana nesa.
Barkanku da wannan rana ta Juma’a da fatan kowa zai yi juma’a lafiya, ko kuma fatan an sakko lafiya. Kafin na je ga sakonni masu karatu zan fara mika sakon barka da juma’a ta zuwa ga ‘yan’uwana da abokan aikina, Sakon barka da juma’a zuwa ga Editana Abdulrazak Yahuza Jere tare da sauran ma’aikatan wannan gida na Jaridar Leadership Hausa baki daya.
- Ana Jimamin Mutuwar Sarauniyar Giwaye Mai Shekara 65 A Kenya
- NDLEA Na Neman Wani Dillalin Kwayoyi Ruwa A Jallo A Jihar Legas
Sakon Barka da Juma’a ga Fadila Aliyu Musa, da ‘Yan tawagar Shafin Taskira fatan kowa yana cikin koshin lafiya, fatan kuma an yi sallar juma’a lafiya. Yanzu kuma zan je ga sakonnin da aka aiko kamar haka:
Assalamu alaikum. Fatan alheri ga wannan fili namu mai tarin albarka, Allah ya daukaka wannan Jaridan tamu a Duniya baki daya. Gaisuwar Goron Juma’a ga makusantana kamar su Abubakar Shuaibu, sai kuma Maharazu Shuaibu, tare da Fatima Shuaibu, da kuma Halima Shuaibu, da Yusuf Shuaibu, sai kuma Usman Shuaibu, daga karshe ina mika sakan Goron Juma’a ga Kakan mu Hannatu Shuaibu. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka da Juma’a.
Daga Ubale Shuaibu Badarawa, Kaduna.
08022179656
Dubun gaisuwa tare da fatan alheri ga wannan Jarida tamu mai tarin albarka. Ina so in mika gaisuwar Goron Juma’a ga makusantana kamar su Alhaji Murnir Wanbai, sai kuma Alhaji Sulaiman Garki, tare da Malam Abdullahi mai sayar da katin waya a Garki, da Alkali Badarawa Kaduna, daga karshe ina mika sakon Goron Juma’a ga Tijjanin Alhaji Nura dake Garki Abuja. Dafatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin. Barka da Juma’a.
Daga Malam Zilkibilu Garki, Abuja.
07034661195
Gaisuwar Goron Juma’a cike da farin ciki ga dangina Hassan Yusuf da ke karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna, da Shehu Umar Kagarku, sai kuma Shehu Yusuf Kagarko, tare da Abdul’Aziz Abdullahi Kagarko, da Zakari Isma’il, daga karshe ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga Malam Falalu Abdullahi da ke garin Abuja. Da fatan duk suna nan lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka da Juma’a.
Daga Isma’il Yusuf, Kagarko.
08168499372
Salam, ina mai mika sakon Goron Juma’a ga manyan abokanaina Malam Bala wanda ya ke garin Zaria inkiya dan kasa nagari, sai kuma Raheenah Masaka da Ikleemacy, tare da Anti Hanane, da kuma Masoyiyata wato Fatima da Muhammad Idris, daga karshe ina mika gaisuwar Goron Juma’a ga Mahaifaya ta A’sha Baffa. Da fatan duk suna cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, Amin. Barka da Juma’a.
Daga Aliyu Muhammad(Tsun-tsun soyayya), Bauchi.
07060664230
Bayan gaisuwa mai tarin albarka, tare da fatan Allah ya daukaka wannan gidan jarida ta mu, nake mika gaisuwar Goron Juma’a ga abokan arziki kamar su Salis Kalifa Baba Ahmad, sai kuma babban aminina wato Muhammad wanda aka fi sani da Mamman a cikin garin Kaduna, da kuma Barista Muhammadu Tasi’u Sirajo, da Yunus Abubakar da ke Kaduna, sai Malam Uwaisu Buhari Imam a Abuja, da kuma Muhammad Idris a Lake Biew Homes Phase 2 a Kado, daga karshe ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga mai gidan na Raji Musa Yakubu. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin. Barka da Juma’a.
Daga Yusuf Shuaibu, Abuja.
08034980391
Da farko, ina farin ciki tare da godiya ga wannan fili na Goron Juma’a, ina so a mika gaisuwar Goron Juma’a ga yarana Zainaf Ahmad, tare da Adam Ahmad, sai kuma Sadik Ahmad, da Halima Ahmad, sai Yusuf Ahmad, da Maimuna Ahmad, tare da Siyama Ahmad, sai Uwar Gida sarautar Mata Madam Suwaiba, da kuma Nasiru wanda ya tafi Saudiyya da iyalansa, tare da Sa’idu Gulu a karamar hukumar Rimin Gado a garin Kano, sai kuma Alhaji Nura a karamar hukumar Kabo, da Isa Reza a garin Masanawa Kabo, da kuma Yakubu Garo, daga karshe ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga Majidadin Kofa Bala Ibrahim. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin.
Daga Shugaba Ahmad Namalan Kazode, karamar hukumar Kabo.
08034041022
Assalamu alaikum. LEADERSHIP Hausa, ina farin ciki da samar mana da dama domin mu sada zumunci ga ‘yan’uwa da abokan arziki. Allah ya kara wa wannan Jaridan tamu farin jinni da daukaka a fadin Duniya daki daya. Da farko, ina mika sakon Goron Juma’a ga masoyana kamar su Babiyanas Gudurega, sai kuma Dogo na garejin Bola Ijora, da Salisu Baturan Gona, da kuma Yahaya Kajiji da Kabiru Muhammad Shuaibu, sai Gali Baffa Agege, da Malam Musa Aram, daga karshe ina mika sakon Goron Juma’a ga Alhaji Sadiku Umar Faki. Da fatan duk suna cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka Juma’a.
Daga Alhaji Jinjiri Mile 12, Legas.
09023489162