A yayin da kakar zaben Shekara ta 2023 ke kara karatowa tukunyar siyasar Jihar Kano sai kara tafarfasa ta ke, Jam’iyyar APC ita ce Jam’iyyar dake rike da madafun ikon Gwamnatin Jihar Kano, wanda hakan yasa duk abinda ta dama haka za a karba a sha.
Amma hakan bai hana kunnowar wata gagarumar wuta wadda idan ba a yi hankali ba ka iya kai jam’iyyar kasa akakar zabe mai zuwa, musamman ganin wata gagarumar matsala ta kunno kai a lokacin wani babban taron Jam’iyyar APC a Kano da aka gudanar ranar Litinin data gabata, wanda shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai ta tarayya Alhassan Ado Doguwa ya yi musayar yawu da dan takarar mataimakin Gwamna na Jam’iyyar APC Alhaji Mutala Sule Garo.
Taron wanda aka gudanar a gidan Mataimakin Gwamna Dakta Nasiru Yusif Gawuna, wanda aka shirya domin tattauna nasarori ko akasin haka kan ziyarar dan takarar kujerar Shugabancin kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya Kawo Jihar Kano a makon da ya gabata.
Sa toka da katsin ta faru lokacin da Doguwa wanda baya cikin wadanda aka gayyata zuwa ganawar, yaje wurin domin ganin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas.
Wata majiya data bukaci a sakaya sunanta ta bayyana wa Jaridar LEADERSHIP Hausa cewa, Ado Doguwa ya fara yin korafi kan cewa shugabanni Jam’iyya basa sashi a duk wani al’amari da ya shafi kudi, amma kuma ana gayyatarsa aiwatar da duk wani aiki mai wahalar aiwatarwa.
Alhassan Ado Doguwa da farko ya fara musayar magana kai tsaye da Mataimakin Gwamna kafin ya koma kan Murtala Sule Garo. Wanda ya yi korafin cewa Murtala ne ya umarci yaransa da su yage fastocinsa a lokacin zuwan Tinubu Kano, wanda kuma a zahirin gaskiya Murtala bai san komai kan haka ba.” Inji majiyar.
A wannan lokacin Murtala ya yi kokarin jawo hankalin sa, tare da nuna masa illar irin wannan dabi’ar tasa tare da tuna masa yadda ya zagi iyayensa (Murtala) a daren jiya lokacin taron da aka gudanar a Gidan Ado Alhassan dake rukunin gidajen Kwankwasiyya.
Sakamakon kalubalantar da Murtala Garo ya yi masa, Ado Doguwa ya rarumi kofin shayin Dake gaban Mataimakin Gwamna tare da jifar Garo dashi. Kamar yadda aka rawaito a kokarin kare wannan farmaki da hannunsa ne gilashin kofin da ya fashe ya samu Garo a hannu.
Baya ga abinda ya faru a ranar Litinin an rawaito cewa Doguwa ya zargi kwamishinan yada labaran Jihar Kano Malam Muhammad Garba da kin sanya sunan sa cikin jerin wadanda za su gabatar da jawabai a lokacin kaddamar da Littafin Gwamna Ganduje a Abuja kwanan nan.
Haka kashegarin waccan tataburza, Alhassan Ado Doguwa ya kara yi wa kakakin Jam’iyyar APC na shiyyar Arewacin Kasarnan Ahmed Aruwa mahangurba, ana tsaka da wannan sai labari ya kara bayyana cewa Doguwar ya naushe Wakilin Jaridar Leadership a lokacin taron manema labarai da ya kira agidansa.
Sule Garo Ya Zargi Doguwa da Laifin farmakarsa da kofin shayi
A nasa bangaren dan takarar kujerar Mataimakin Gwamna na Jam’iyyar APC Alhaji Mutala Sule Garo ya zargi Shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai ta Tarayya Ado Alhassan Doguwa da laifin jifarsa da kofin shayi. Lamarin dai ya faru Ranar Litinin din makon da ya gabata a Gidan Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna.
Garo ya ce, “lokacin da Doguwa ya kutsa kai cikin dakin taron ya nuna rashin amincewarsa da kin gayyatarsa wurin taron domin a cewarsa wannan lokacin rabon kudi ne, amma idan da ace wani aiki ne mai wahalar aiwatarwa ga Jam’iyya da su za a gayyata.”
“Doguwa na zargina da lalata fastocinsa wanda ni kuma na musanta haka, wanda hakan yasa ya rarumi kofin shayi dake gaban Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya jefe ni dashi.” In ji Garo.
Amma dai Shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai ta Tarayya ya musanta cewar shi ne ya farmaki Sule Garo da Kofin shayi.
Ba Na Daukar Zagi Da Cin Zarafi -Doguwa
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai ta Tarayya, Alhassan Ado Doguwa ya Magantu kan batun arangamarsa da dan takarar kujerar Mataimakin Gwamna na Jam’iyyar APC a Kano, Murtala Sule Garo, wanda hakan ne ya haifar da rikici tsakanin su.
Da yake yi wa Manema labarai karin haske kan lamarin ranar Talatar data gabata, Shugaban masu rinjayen na Majalisar wakilai ta tarayya ya musanta cewa yaje wurin taron Jam’iyyar domin rikici da Garo, ya ce yaje wurin ne domin ganawa da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano Abdullahi Abbas. Haka kuma Doguwa ya musanta cewar da ake ya ji wa Garo rauni lokacin da lamarin ya faru.
Ya ce, “banje wurin domin halartar taron da ake ba, naje kawai domin naga Shugaban Jam’iyya Abdullahi Abbas na wuce.”
“Lokacin da na isa gidan Gawuna sai na shiga dakin da ake taron, na iske ana tattaunawa. Sai na yi barkwanci da Mataimakin Gwamna, inda na ce kamata ya yi Majalisar Wakilai ya kasance tana da wakilci a wannan taro.
“Kawai sai Murtala ya katseni yana mai cewa ‘dole ne sai an gayyace ka, dole ne sai an gayyaci wani Wakilin Majalisar Wakilai? Daga nan sai ya fara zagina yana muzantani, yana cewa “Banza marar mutunci, dole ne a gayyace ka?”
“Ban mayar da martani ba domin ina da kyakkyawar tarbiyya, sai ya ci gaba da zagina harma yake kokarin yaga min riga, anan ne na fusata na fara mayar masa da martani”
“Harma sai da ya yi kokarin cimin kwala, a kokarin kara kusanto ni ne domin yin fada dani, akwai kofin shayi a kan tebur, Saboda haka sai Garo ya bugi kofin ya fadi kasa kuma ya fashe.
“Lokacin da ya zaburo gareni, sai ya zame a kasa kuma ya fada kan wannan fasasshen Kofin wanda shi ne ya yi masa rauni, ni ban yi wa Garo rauni ba. Inji Shi
“Wannan shi ne yadda aka mayar da labarin cewar na ji wa Garo rauni, amma ni banji masa rauni ba. Ban yi amfani da wani abu ba wanda zai iya cutarwa,” Inji Doguwa.
Sai dai cikin jawabin nasa ya tabbatar da cewa shi ba zai jure duk wani nau’in zagi gareshi ba, Doguwa ya kira Gwamna Abdullahi Umar Ganduje domin ya yi kokarin shawo kan matsalar da Jam’iyya ke ciki kafin ta nutse a Shekara ta 2023.
Alhassan Ado Doguwa ya Jadadda aniyarsa na ci gaba da goyon bayan takarar Dakta Nasiru Yusif Gawuna tare da nasarar Jam’iyyar APC a Jihar Kano.
Al’amarin na cin zarafin wakilin jaridar Leadership a Kano, Abdullahi Yakubu, a ranar Litinin da ta gabata ya faru ne lokacin da shi wannan dan Majalisa dake wakiltar kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa a Majalisar Tarayya, ya kira taron manema labarai domin fadar nasa labarin kan takaddamar da aka ce ta wakana tsakaninsa da dan takarar mataimakin Gwamnan Kano a Jam’iyyar su ta APC, Alhaji Murtala Sule Garo, a yayin wani taro a karshen makon da ya gabata, inda har ta kai shi dan majalisar ya raunata Murtalan.
Shima Abdullahi Yakubu, wakilin jaridar Leadership a Kano, ya fuskanci makamancin wannan yanayi na Murtala, koda yake marin shi ta bayan kunnen sa aka yi, sanadiyyar yunkurin bada shawara da ya yi kan wasu kalamai daya ji sun fito daga bakin Alhassan Ado.
Wannan lamari ne yasa Wakilin Jaridar Leadership din yaga ba zai yiwu kawai ya bar wannan lamari haka ba, wannan tasa ya garzaya gaban kuliiya domin neman hakkinsa kan wannan lamari. Wannan yasa alkalin kotun ya umarilci Shugaban shiyya ta daya ta rundunar ‘yan sanda dake Kano da su gudanar da bincike kan wannan lamari.
Ba tare da bata lokaci ba Mataimakin sifeton ‘yan sandan Nijeriya mai kula da shiyya ta daya da ke Kano ya umarci kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano ya gudanar da kwakkwaran bincike game da cin zarafin da shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan Nijeriya, Alhassan Ado Doguwa, ya yi wa wakilin jaridar LEADERSHIP.
SP Abubakar Zayyanu Ambursa, kakakin shiyya ta daya ta rundunar ‘yan sandan Nijeriya da ke Kano, ya tabbatar da samun takardar umarnin daga kotun Majistire dake Gyadi-Gyadi a Kano kuma ya ce tuni Mataimakin Babban Sifeton ‘yan sandan ya mika takardar ga kwamishinan ‘yan sanda na Kano tare da ba shi umarnin gudanar da cikekken bincike game da lamarin.
Sai dai kuma kungiyoyin rajin shugabanci na gari da tabbatar da demokaradiyya a Nijeriya sun ce akwai bukatar ‘yan sanda su gudanar da sahihin bincike akan wannan batu.
Kwamrade Abdulrazak Alkali daraktan kungiyar OCCEN masu wayar da kan jama’a kan harkokin dimokaradiyya, ya ce akwai bukatar ‘yansanda su yi abin da ya kamata akan wannan batu, la’akari da muhimmancin rawar da ‘yan jarida ke takawa ga ci gaban dimokaradiyya.
A nata bangaren, kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ba zata lamunce da wannan aika-aika a kan ‘ya’yan ta ba. Kwamrade Abba Murtala Sakataren reshen Jihar Kano na kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya NUJ, ya ce sun kafa kwamiti domin gudanar da kwakkwakwaran bincike kuma za su tabbatar da karewa tare da kwato hakkin dan kungiyar tasu.
A wani labarin kuma, wasu matasa sun yi aikin kakkabe kusan dukkanin manyan allunan da ke dauke da hotunan dan takarar Gwamnan Kano karkashin inuwar Jam’iyyar APC Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da na mataimakinsa, Murtala Sule Garo. Matasan sun bi manyan titunan birnin Kano da sauran muhimman wurare da aka kafa irin wadannan alluna.
Sai dai kuma da yammacin ranar wannan Litinin din Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje tare da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas sun Jagorancin wani taron sulhu da aka gudanar a Abuja, Gwamnan ya bukaci ‘ya’yan nasa biyu Mutala da Doguwa dasu yafe wa juna tare da yin musabiha. Hakan kuma akayi.
A cikin wani faifan sautin da Jaridar LEADERSHIP Hausa ta saurara, an ji shugaban masu rinjayen Alhassan Ado Doguwa na tabbatar da wannan sulhu harma ya nemi gafarar duk wanda ya sabawa, sannan ya tabbatar da ci gaba da yi wa Jam’iyyar APC hidima da ‘yan takarkarun Jam’iyyar tun daga sama har kasa.
Amb. Mansur Haruna Dandago gudane cikin masu kallon abinda Alhassan Ado Doguwa a mtsayin rashin yi wa Allà h godiya, domin a cewarsa duk wanda ke kan kowacce irin Kujera ce Kano albarkkcin Muratala Da Gawuna yake ci, domin ba don jajircewar da suka nuna a lokacin ‘Inconclusibe’ ba da yanzu ba wannan maganar ake ba. Idan kuwa haka me dole durkusawa Wada ba gajiyawa bane.
Cikin wadanda Suka bada gudunmawa har wannan sulhu ya tabbata akwai Sanatan Kano ta Kudu Kabiru Ibrahim Gaya, Dan takarar Shugabancin kasa na Jam’iyyar APC Ahmed Bola Tunibu, Gwamnonin Katsina Birnin Kebbi da Zamfara.
Yanzu haka dai murna ta komawa wasu Jam’iyyun Adawa da Suka kimtsa domin idan anyi bari su kwashe, musamman Jam’iyyar NNPP wadda acikin wasu Kalaman Doguwa akaji yana yabon jagoran Kwankwasiyya wanda akayi zaton ungulu na shirin komawa gidanta na tsamiya.
Yanzu abinda ya rage shi ne a gani a kasa wai da akace ana biki a gidansu ya ce mu gani a kasa, masu nazari tare fashin baki a harkokin siyasar Kano sun zuba na mujiya suga yadda wannan sulhu zai tabbata domin ci gaba da yin tafiya tare.