Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya bukaci Sarkin na Katagum, Alhaji Umar Faruk II, da ya bi sawun iyayensa da kakaninsa wajen tafiyar da harkokin sarauta domin kyautatawa da inganta rayuwar al’umar masarautarsa ta Katagum.
Ya kuma bukaci sarakunan gargajiya a jihar da su kaurace wa tsoma bakinsu cikin harkokin siyasa, a maimakon hakan ya nemi da su rungumi matakan da iyayensu suka dauka na hidimta wa jama’a.
- Gwamnan Bauchi Ya Amince Da Fitar Da Miliyan 500 Don Biyan Giratuti
- Asirin Kwalejojin Ilimi 41 Da Ke Ba Da Shaidar NCE Ta Bogi Ya Tonu A Bauchi
Da ya ke mika sandar girma ga sarkin Katagum a garin Azare ranar Asabar, Gwamna ya ce sarkin Katagum na 12 ya kasance mai kokari wajen bunkasa lamuran da suka shafi tattalin arziki, tsaro da ci gaban al’umar masarautar, ya bukaci da ya kara azama ta hanyar amfani da gogewarsa saboda kara samun inganta al’amura a masarautarsa, jihar Bauchi da ma kasa baki daya.
Mika sandar girman na zuwa ne bayan shekara biyar da nadin Sarkin na Katagum wanda tsohon gwamnan jihar Bauchi, Muhammad A. Abubakar (SAN), ya yi, biyo bayan zabinsa da masu alhakin zabar sabon sarki suka yi.