Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya sha alwashin cewa zauren majalisar dattawan Nijeriya zai yi kokarin tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta tallafawa harkokin kiwon dabbobi a kasar nan- a matsayin sa na daya daga cikin manyan ginshikan ci gaban tattalin arzikin kasar nan.
Sanata Lawan ya sanar da hakan a karshen mako, a sa’ilin da yake kaddamar da allurar riga-kafi ga dabbobi kyauta a kauyen Jajuwa dake karamar hukumar Jakusko a jihar Yobe; shirin da Gidauniyar SAIL Foundation a karkashin sa ke daukar nauyin gudanar dashi tun shekarar 2018, domin al’ummar mazabar sa.
Ya ce harkokin kiwo a Nijeriya ba kashin yasarwa bane, a matsayin sa na daya daga cikin manyan kadarkon da ke dauke da tattalin arzikin Nijeriya, “wanda kuma ya dace gwamnati ta tallafa wa harkar kiwo, saboda muke cin gajiyar fanni wajen ci gaban tattalin arzikinmu, sannan barin sa haka ba tare da agaza wa bangaren ba, to ba a yi masa adalci ba; duk sana’a ce mai zaman kanta, dole a tallafa wa sashen.”
“A hannu guda kuma, suma bankuna harkar sana’a ce mai zaman kanta, wanda idan har gwamnati za ta tallafa wa masu tafiar dasu ba, ban ga dalilin da za a ki tallafa wa makiyaya dabbobi ba, wanda a zahiri ma sune suka fi kowa cancanta a tallafa musu, musamman gwamnatin tarayya.”
Sanata Lawan ya kara da cewa, “Zamu ci gaba da matsa wa Gwamnatin Tarayya lamba har sai ta tallafawa Fulani makiyaya dabbobi domin rage matsalolin da su ke fama da su lokaci zuwa lokaci.”
“Sannan a kokarinmu, a yau mun zo nan ne domin kaddamar da allurar rigakafin dabbobi, wadanda suka kunshi shanu, tumaki, da awakinmu, tare da sauran kananan dabbobi a wannan shiyya ta Yobe ta Arewa.”
“Wannan biki ne wanda muke gudanar dashi kowace shekara domin yiwa dabbobi allurar riga-kafin cutuka daban-daban, wanda a bara mun yi wa dabbobi kimanin miliyan daya da rabi, kuma a wannan shekara ma haka zamu yi. Sannan zamu kara da bai wa Fulaninmu tallafin dusa da sauran abincin dabbobi kyauta, domin rage musu wahalhalu.”
Bugu da kari, Sanata Lawan ya kaddamar da shirin bai wa al’ummar yankin sa tiyata kan matsaloli daban-daban kyauta, wanda ake gudanar dashi tun shekaru biyar da suka gabata, a asibitin kwararru na jihar Yobe dake Gashua, da Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) ta Nguru.
Ya ce tallafin ayyukan jinya kyauta domin masu fama da rashin lafiyar ido, tiyata kaba, duba lafiyar mata da yi wa wasu tiyata, gwajin cutar dadji, da sauran su, duk a kyauta ga kimanin mutum 5000.
Har wala yau, Sanata Lawan ya yi alkawarin gina Cibiyar kula da masu fama da cutar koda a Asibitin Kwararru ta Gashuwa domin saukake wa jama’ar yankin wahalhalun cutar. Kana da sake gyara hanyar Kwanar-Baderi zuwa Gir-gir, hanyar mota tare da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a sabuwar Sakandare Gwamnatin Tarayya dake Gashuwa, da sauran muhimman ayyuka a ziyarar da ya kai ta kwanaki uku a Yobe ta Arewa.