Yayin da ake kara kusantar zabe a Nijeriya, jam’iyyun siyasa da wadanda su ka fito takara a mukamai na ci gaba da yada manufa tare da bayyana irin kyawawan manufofin da suke burin aiwatarwa, idan sun kai ga nasara a zaben shekarar 2023 da ke tafe.
A Jihar Kano, da ta zama cibiyar siyasar Nijeriya, akwai masu neman kujerar gwamna a jam’iyyu daban-daban kuma ake jin duriyarsu da kuma bayyana wa Kanawan irin tanadin da suka yi musu idan su ka kai ga nasara.
- Gobara Ta Kone Shaguna 15 Da Lalata Kaya Na Miliyan 19 A Jihar Kwara
- Gobara Ta Yi Barna A Kasuwar Sayar Da Kayan Masarufi Ta Singa Da Ke Kano.
Jami’yyar APC ce ke mulkin Jihar Kano, inda suke da Dakta Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin dan takara, sai kuma jami’yyar NNPP ta tsohon gwamna Rabi’u Kwankwaso da suke da Abba Kabiru Yusuf da kuma jami’yyar PDP da suke da Sadiq Aminu Bashir Wali a matsayin wanda zai yi wa jam’iyyar takara a 2023.
Wali, wanda tsohon Kwamishinan albarkatun ruwa ne a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, ya zama dan takarar gwamnan ne a jam’iyyar PDP bayan da ya yi nasara a zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar.
Tun da farko jam’iyyar PDP a Kano ta fuskantar rikici a kan wane ne halastaccen dan takarar gwamnan a jami’yyar.
Muhammad Abacha da Sadiq Aminu Wali kowane a cikinsu na jin shi ne halastaccen dan takarar jam’iyyar, biyo bayan rikicin zaben fidda gwani da kowanne bangare ya gudanar karkashin sa idon hukumar zabe ta kasa INEC.
Shugabancin jam’iyya bangaren Shehu Wada Sagagi, ya gabatar da zaben fidda gwani na jam’iyyar kuma a matsayarsa, Muhammed Abacha ne ya samu nasara.
Bayan zuwa kotu da aka yi, kotu ta sake ayyana Sadiq Wali a matsayin halastaccen dan takarar da zai yi wa PDP takarar gwamna a Kano.
Sai dai duk da wannan damar da Wali din ya samu amma har yanzu ya gaza fitowa fili ya bayyana wa Kanawa manufofinsa da kuma irin tanadin da gwamnatinsu ta yi musu idan ya kai ga nasara.
Haka kuma wani abin mamaki ga lamarin Sadiq Aminu Wali, shi ne yadda ya ke biris da gayyatar da manyan kungiyoyi ke shirya wa ‘yan takarar gwamna a Kano, inda al’umma suke kallon ko bai shiryawa takarar ba.
Haka zalika, ko a lokacin da Sadiq Wali din ya ke Kwamishinan ruwa na Kano, babu wani abin a zo a gani da ya tabuka domin sai da ta kai ga yara ‘yan makaranta ba sa samun zuwa makaranta ko kuma ba sa zuwa da wuri sakamakon fadi-tashin neman ruwa.
Masu sharhi a kan al’amuran siyasar Kano da sauran ‘yan siyasar jihar, sun dade da bayyana Sadiq Aminu Wali, a matsayin dan gatan da bai san wanne hali talaka a Jihar Kano ke ciki ba, kuma ba shi da wani kuduri ko manufa da zai ciyar da Kano gaba idan ya zama gwamna a 2023.
Mafi yawan al’ummar Jihar Kano na kallon Sadiq Aminu Wali a matsayin “Sabon Yankan Rake” a siyasa domin ba shi da wata kwarewa ko gogewar da zai ja ragamar shugabancin Jihar Kano da ke da sama da mutum miliyan tara.
Kuma shi ma ya tabbatar wa da duniya hakan la’akari da yadda ya gaza fitowa fili ya tallata takararsa da manufofinsa ga Kanawa.
Babu shakka ya zama wajibi ga al’ummar Jihar Kano da su zabi jajirtaccen mutumin da ya ke da ilimin addinin Islama da kuma na zamani tare da gogewar aiki da kuma manufa wanda ya ke da sanayya tsakanin manyan ‘yan kasuwa da ‘yan boko da ma’aikatan gwamnati da kuma goyon bayan kungiyoyin fararen hula, ba wai su bi rububi wajen zabar “Yankan Rake” ko dan gatan da bai san daga ina zai fara magance matsalolin da su ka yi wa jihar katutu ba.
Buhari Abba dan jarida ne ya rubuto daga Kano, Najeriya