Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya ce ya daina karanta labarai a shafukan sada zumunta.
Tinubu, wanda akai-akai yana sabunta ingantattun hanyoyin sadarwar sada zumunta da sunansa, ya bayyana hakan a cikin wani faifan bidiyo da aka yada.
- Yadda Za A Tsaftace Hammata Da Cinyoyi Su Yi Kyau
- Zamantakewar Aure Tsakanin Miji Da Mata: Wa Aka Fi Zalunta?
“Ba na duba kafafen sada zumunta; suna daga min hankali. Idan na karanta, nakan sa jinina ya hau sannan na fusata. Ba na karanta komai a can, don haka idan ina son jin wani abu; ‘Ya’yana ko ma’aikatana ke wannan, idam na gaji, sai na ce don Allah a manta da komai!”
Tinubu, wanda ke kan gaba a yakin neman zaben 2023, ya ce kafafen sada zumunta na daga masa hankali.
Yayin da yake karkare jawabinsa a gangamin yakin neman zabensa da aka gudanar a Jos a ranar Talata, ya sha fama da zamewar harshe yayin da ya yi kuskuren yi wa jam’iyyar PDP addu’a a lokacin da ya ke kokarin ambaton jam’iyyarsa.
Hakan dai ya jawo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta yayin da masu suka suka yi wa dan takarar jam’iyya mai mulki suka ce bai cancanci zama shugaban kasa ba.