Akalla ‘yansanda uku ne ake fargabar sun mutu a ranar Asabar a lokacin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari a shingen bincikensu da ke Agbani, hedikwatar karamar hukumar Nkanu ta Yamma a Jihar Enugu.
Wasu da dama kuma sun jikkata yayin harin, wanda ya faru a wani zagaye da ke kusa da ofishin ‘yansanda na yankin Agbani.
- Fara Yakin Neman Zaben APC: Wacce Alkibla Tinubu Ya Dosa
- Tinubu Ya Amince Da Sa’adu Gulma A Matsayin Shugaban ‘Yan Arewa Na APC A Legas
Jami’an ‘yansandan na cikin aikin bincike ne lokacin da maharan suka hango su, nan take suka bude musu wuta, inda suka harbe jami’an tsaro uku.
‘Yan bindigar sun kai harin ne a cikin wata mota, kuma an ce sun tsere zuwa Ugbawka.
Harin dai ya faru ne kasa da sa’o’i 24 bayan wasu ‘yan bindiga suka kashe tsohon kwamishinan jihar kuma shugaban karamar hukumar Oji-River, Cif Gabriel Onuzulike da kuma kanensa a garinsu na Nkpokolo-Achi.
A halin da ake ciki kuma, rundunar ‘yansandan jihar Enugu ta bayyana cewa, biyo bayan kai daukin gaggawa kan lamarin da ya faru a Oji-River, sun kama wasu mahara biyu tare da kashe su daga hannun ‘yansanda da rundunar hadin gwiwa.
Daniel Ndukwe, kakakin rundunar ‘yansandan jihar ne ya bayyana hakan.
Ya ce rundunar ta kwato bindiga kirar AK-47 dauke da kunshin harsasai biyu dauke da alburusai, mota kirar Toyota Land Cruiser Jeep da mota kirar Toyota Camry da kuma RAV4 Jeep.