A ci gaba da bayyana manufofin gwamnatin da zai kafa idan ya yi nasara, ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin damƙa manyan ayyukan raya ƙasa a hannun kamfanoni masu zaman kan su, ta yadda zai sauƙaƙe wa Gwamnatin Tarayya nauyi da wahalhalun kashe maƙudan kuɗaɗe wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa.
Atiku ya bayyana haka a taron ganawar da ya yi da Kungiyar Editocin Najeriya a Legas.
“Idan ku ka kalli irin gagarimin ayyukan da ke gaban gwamnati a ƙasar nan, kamar gina tashoshi jiragen ruwa, gina hanyoyin jiragen ƙasa, to ana buƙatar maƙudan kuɗaɗe ne. Kuma kun dai san a yanzu gwamnati ba ta da waɗannan kuɗaɗen,” inji shi.
“Har gara a damƙa waɗannan ayyuka ga kamfanoni masu zaman kan su, a zaftare ko a cire masu haraji. A gina manyan ayyukan da kuɗaɗen su, sannan su kula su karɓi kuɗaɗen da su ka kashe wajen gudanar da ayyukan. To ya haka ne za mu samu ci gaba, bunƙasa, samar da ayyukan yi da kuma samun yalwar arziki a faɗin ƙasar nan.”
A wurin taron dai Atiku ya yi alƙawarin ɗaukar ‘yan sanda 500,000, sojoji 500,000.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023 Atiku Abubakar, ya ƙudiri aniyar ɗaukar sojoji da ‘yan sanda milyan ɗaya idan ya zama shugaban ƙasa.
Sannan kuma ya ce za a wadatar da su da ingantattun kayan aiki tare da ba su horo, domin samar da tsaro, aikin yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Atiku ya yi wannan alwashin a lokacin da ya ke ganawa da shugabannin Kungiyar Editoci ta Ƙasa (NGE), a Legas, a ranar Laraba.
Ya ce wannan ƙudiri na cikin ajandojin sa biyar muddin ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023.
Ajandar sa ta biyu kuwa cewa ya yi ita ce farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa wanda kowa ya san ya taɓarɓare.
“Na ƙudiri aniyar ci gaba da irin tsarin da mu ka yi tsakanin 1999 zuwa 2007, lokacin ina mataimakin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo. Za mu bai wa kamfanoni masu zaman kan su damar samun sauƙin ayyukan bunƙasa tattalin arziki.”
Daga cikin abin da zai yi wa kamfanonin, Atiku ya ce zai rage masu haraji ta yadda za su riƙa yin manyan ayyukan raya ƙasa, kamar gina tashoshin ruwa, manyan titina, hanyoyin jiragen ƙasa da sauran manyan ayyuka masu cin kuɗaɗe sosai, “musamman tunda gwamnati ba irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe gare ta ba.
“Saboda zan zaftare wa kamfanoni da masana’antu haraji, ta yadda su kuma za su riƙa gina manyan ayyukan raya ƙasa, waɗanda ke buƙatar kashe maƙudan kuɗaɗe kafin aikwatar da su.”
Atiku ya ce zai rungumi kowane yanki ba tare da nuna bambanci ko fifiko ba. Ya ce fifikon wani yanki da wannan gwamnatin ta riƙa bayarwa wajen raba muƙamai ba zai faru a gwamnatin sa ba, idan ya zama shugaban ƙasa.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Aminu Tambuwal, mai suna Mohammed Bello ya fitar bayan ganawar, Daraktan Kamfen ɗin Atiku/Yakuwa 2023, wato Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, ya jinjina wa NGE da Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta Ƙasa (NUJ) wajen jajircewar su domin ganin dimokraɗiyya ta ɗore a ƙasar nan. Ya ce Atiku a shirye ya ke ya fara aiki wurjanjan da zaran an zaɓe ya zama shugaban ƙasa.