Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, a ranar Litinin ya karbi bakuncin wani jigo a jam’iyyar PDP, Haladu Mohammed, zuwa jam’iyyar APC.
Mai taimaka wa Gwamna Buni kan harkokin yada labarai, Mamman Mohammed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.
- Mata Da Yara Akalla 721 Aka Yi Wa Fyade Cikin Watanni 9 A Kano
- Ganduje Ya Amince Da Kammala Titin Garin Kwankwaso Da Sauran Wasu Aiyuka A Kano
A cewar sanarwar, babbar jam’iyyar adawa a Jihar Yobe na ci gaba da tabarbarewa, wanda hakan ke barazana ga mambobin jam’iyyar da tuni suka yi kasa a gwiwa.
“Jam’iyyar ta rasa Alh. Abbagana Tata, tsohon shugaban jam’iyyar kuma mai neman takarar gwamna da Hajiya Masafaram, jarumar siyasar Yobe ta Arewa, wadanda suka sauya sheka tare da dubban magoya bayansu zuwa APC.
Sanarwar ta kara da cewa “Tata da Masafaram sun kasance ‘yan PDP masu biyayya tsawon shekaru 23 amma sun koma APC domin marawa gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni baya wajen gina jihar.”
Sanarwar ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar da suka rage suma sun nuna sha’awarsu ta komawa APC.