‘yan bindigar da suka yi garkuwa da tawagar ‘yan biki Mutum 30 a Hanyar Sokoto zuwa Gusau sun fara tuntubar iyalan wadanda abin ya shafa.
Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato, wadda a kasarta lamarin ya faru, har yanzun ba ta ce uffan ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Sanusi Abubakar, yaki daukar waya ballantana ya maido da amsar sakonnin da aka tura masa domin tabbatarwa da karin bayani kan lamarin.
Sai dai Sakataren Kungiyar Sadarwa ta Jihar Zamfara Ashiru Zurmi ya ce “An yi garkuwa da mambobin 30, kuma har yanzu suna tsare. Sai dai an yi sa’a, ‘yan bindigar sun yi amfani da wayoyin wadanda suka kama (Mutum biyar) sun kira mu; kawai sun sanar da mu cewa suna tare da su”.
A cewarsa, babu wani kudin fansa da barayin suka nema.
Ku tuna cewa akalla mutane 30 ne rahotanni suka ce an yi garkuwa da wasu ‘yan tawagar biki suna dawowa daga taron biki a karamar hukumar Tambuwal ta jihar Sakkwato da yammacin ranar Asabar wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da motocin su a kan hanyar Sakkwato zuwa Gusau.