Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tawagar kwallon kafar Morocco, Atlas Lions, da mai mulkin kasar, Sarki Mohammed na VI murnar kafa tarihi inda ta zama kasa ta hudu a Afrika da ta taba tsallakawa zuwa zagaye mai kasashe takwas (Quarter final) na gasar cin kofin duniya kuma ta farko da ta samu gurbin zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya na FIFA 2022 da ke gudana a Qatar.
Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar, ya ce kasar Morocco tasa daukacin kasashen nahiyar alfahari sabida kwazon su, kuma sun nuna cewa kasar Afirka za ta iya lashe gasar kofin na duniya da ake yi a Qatar.
Shugaba Buhari ya yabawa kungiyar bisa kwarewa da aikin hadin gwiwa da suka yi, inda ya kuma bayyana cewa ba za a iya cimma hakan ba sai da irin rawar da mahukuntan kasar Morocco suka taka wajen zakulo wadanda suka cancanta da wakiltar kasar a gasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp