Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bai wa Benzema damar komawa tawagar ‘yan wasan Faransa don buga wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya tsakaninta da Argentina.
Dan wasan dai ya ji rauni ne kwana biyu a fara gasar a Kasar Qatar.
- Da Dumi-Dumi: Jakadan Nijeriya A Sifaniya, Demola Seriki Ya Rasu
- Majalisar Dattawa Ta Bukaci CBN Ya Sake Nazarin Dokar Takaita Cirar Kudi
Hakan ta sa dan wasan ya fita daga jerin ‘yan wasan da za su wakilci kasar a Qatar.
Duk da raunin da ya samu Faransa ba ta maye gurbinsa da wani ba, hakan ke nuna cewar dan wasan na iya komawa bayan murmurewa da ya yi a kan lokaci.
Faransa dai ta samu nasarar zuwa matakin wasan karshe bayan doke Morocco da 2 da babu a daren ranar Laraba.
Yanzu haka dai Faransa ta sake zuwa matakin wasan karshe a karo na biyu a jere, bayan lashe kofin a 2018 a Kasar Rasha.
Faransa da Argentina za su buga wasan karshe don fitar da zakara guda daya a cikin, wanda za a nada a matsayin wadda ta lashe gasar.