Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi iya abin da zai iya a matsayinsa na shugaban kasa.
Shugaban Buhari ya bayyana haka ne a Washington lokacin da yake tarbar sakatare janar na Gidauniyar Abu Dhabi, Sheikh Al-Mahfoudh Bin Bayyah da mataimakinsa, Fastor Bob Roberts a kasar Amurka.
“Muna da yawan al’umma wanda muke fuskantar matsaloli, amma muna iya bakin kokarinmu a wasu yankuna masu yawa. A tsawan mulkina na shekaru bakwai da rabi, na yi iya bakin kokarina,” in ji shi.
A cewar mashawarcin Buhari, Garba Shehu ya ce magance matsalolin da suka addabi matasa shi ne abu mai muhimmanci da gwamnati ta dauki alkawarin inganta rayuwarsu.
Buhari ya bayyana abubuwan da ake bukata na daga goben matasa wanda ya hada da kauce wa ta’addacin a kan addini, inda ya bukaci gidauniyar ta ci gaba da mayar da hankali a kan matasa wanda ta dauki alkawarin samar da ci gabansu.
“Aikinmu yana da matukar muhimmanci wajen taimakawa, musamman ga matsa, wanda fahimtar juna a lokaci daya abu ne da muke alfahari da shi wanda muka gada.
“Wannan babbar gidauniya tana taimakon goben matasa wajen kokarin tsara yadda za su rayu cikin kwanciyar hankail. A namu bangaren, za su ci gaba da magance matsalolinmu, musamman ma wadanda suka shafi matasa.”
A nasa jawabin, Bin Bayyah ya bayyana cewa sun zo ne su bayyana wa shugaban kasa tare da gayyatarsa zuwa wajen bayar da lambar karramawa da gidauniyar Abu Dhabi ta ba shi bisa nasarar da ya samu na inganta zaman lafiya da karfafa tsaro.