‘Yansandan jihar Kebbi sun kama masu garkuwa, Angulu da Abdulahi Altu, a jihar Kebbi tare da gano bindiga kirar AK 47 da harsasai guda 47.
Kamar yadda aka bayar da sanarwa ga manema labarai wadda kwamishinan ‘yansandan jihar Ahmed Magaji Kontagora, ya saw a hannu, cewa, wasu gungun masu garkuwa sun dira gidan Alhaji Adamu da ke kauyen Laga da ke karamar hukumar Bagudo suka kama wasu.
Haka kuma takardar ta nuna cewa:” Jin wannan labarin ke da wuya, sai ‘yansanda suka bazama, domin gano inda masu garkuwar suke, sun samu nasanar gano maboyar ta su, inda suka yi musu ruwan-wuta. Sakamakon haka suka samu nasarar kubutar da wanda masu garkuwar suka kama sannan suka samu bindiga AK47 da harsasai da adda.
“An kama wani mutum mai suna Alti Abdullahi da ke Sabon-gari, cikin karamar hukumar Bagudo.
“Lokacin da a’yansanda ke yin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ya bayyana sunan sauran ‘yan kungiyar ta su wadanda suka gudu wato Dogo Bube da Chakari da Jabbi Daneri da kuma Shehu Tambaya.”
Bayanin ya ci gaba da cewa, wanda ake zargin ya ce ya aikata laifin fashin da yin garkuwa da Alhaji Ado da ke kauyen Sanji da Alhaji Muhammadu da ke Tungar Gyado dukkansu a karamar hukumar Bagudo.
Kwamishinan ‘yansandan jihar ya yi bayanin cewa wadanda ake zargin sun karbi tsabar kudi naira miliyan uku da dubu dari biyar, a matsayin kudin fansa, ya ce yanzu haka suna ci gaba da bincike.
Haka kuma ya ce:“Bindigar da suka kama Ak 47 na da wata lamba LZ09119 da harsasai guda 24..”