• English
  • Business News
Tuesday, June 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘PHISHING’ Sabuwar Hanyar Kutse A Facebook, WhatsApp da Asusun Ajiyar Banki

by Ibrahim Sabo
2 years ago
in Rahotonni
0
‘PHISHING’ Sabuwar Hanyar Kutse A Facebook, WhatsApp  da Asusun Ajiyar Banki
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Tun bayan rubutun da ya gabata a wannan filin na Kimiyya da Fasahar Sadarwa, akan yadda mutum zai kare kansa daga masu kwacen Facebook da WhatsApp (Hackers), to har yanzu wasu suna kiran waya a kan wannan matsala, duk da sun saka makullan sirri masu sarkakiya.

Eh lallai babu shakka zuwa yanzu yawaitar kwacen shafin Facebook da WhatsApp din ya yi sauki kadan. Amma har yanzu ana samu kadan-kadan. Ko da kuwa ka saka makullan sirri (password) masu sarkakiya, to za su iya kwace maka shafin naka ta hanyar Phishing.

  • Yadda ‘Hackers’ Ke Amfani Da Hanyar Smishing Wajen Yin Kutse

Mene Ne Phishing?
Phishing wani tarko ne wato wani ‘common technikue’ ne wanda ake amfani dashi wurin kwacen makullan sirri na Facebook da WhatsApp (hacking password) har da asusun ajiya na Banki.
Phishing wata manhaja ce wadda ake cracking da copy na sirrukan masu website, page, da kuma sace wa users password, da labarai masu muhimmanci (sensitive information) kamar katin waya (credit card) da sauransu.

Daga cikin hanyoyin da ‘hackers’ din suke bi don kutse a shafukan mutane, har su kwace shafin ta hanyar Phishing shi ne, suna kirkirar ‘page’ na bogi, wanda ya yi kama da wani shafi na gaskiya. Wato za su kwaikwayi wani shafi su yi ta yada shi (sharing).

Da farko suna dubawa su ga me aka fi damuwa da shi, to sai su bude shafi mai kama da wancan din. Kuma sun fi bude shafi mai alaka da daukar ma’aikata, wanda zai samu tururuwar cike-cike na jama’ar.

Labarai Masu Nasaba

2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

Tsadar Rayuwa: Yadda Al’umma Suka Yi Sallah Cikin Kunci

Mu dauki misali da shafin INEC na daukar ma’aikata da shafin N-Power. Masu kutsen ‘Hackers’ sun bude page a Facebook da website daban-daban duk na bogi da sunan N-Power. Jama’a da dama sun yi rubdugu da tururuwa wajen bin wadannan shafuka, a tunaninsu shafin N-Power ne na gaskiya.

A cikin wadannan shafukan nasu, za su ce ka saka email da password har da lambar waya. Wani lokacin har da lambar BBN suke tambaya. Ta haka za su samu bayananka (details), sai ya zama duk shafukanka na Facebook, whatsapp da asusun ajiyarka na Banki da sauransu duk za su iya kutsawa su shiga.

Mafi yawan mutane ana yaudararsu ne ta hanyar a yi musu abu kyauta (free). Masu Phishing suna kikirar shafin bogi na MTN, Airtel, ko Glo, sai suce ka saka email da password dinka za a baka kyautar “1GB ko 3GB data”. Da zarar ka saka shikenan sun samu bayananka, sai su yi abin da suke so yi da shi. Su kuma mafi yawan mutane suna da son abu na kyauta, to anan kuma, ake rasa muhimman abubuwa.

Kwanan nan hackers din suka yi amfani da manhajar Phishing suka kikiri wani shafin N-Power na bogi a WhatsApp, sai suce ka saka lambar wayarka, idan ka samu N-Power za su sanar da kai. Kowa idan ya saka, to ya samu. Sai su taya ka murna. Sai su ce ka tura a group din WhatsApp guda biyar. Duk abin da ka ji an ce maka ka tura a group biyar ko sama da haka. Kai ko a group daya aka ce ka tura, wannan shafin na bogi ne.

Akwai wani misali da wani ya bayar a kan irin yadda mutane suke son abu na kyauta.
Ya ce “akwai wani mutum ya gina gidan namun Daji (Zoo), sai yace kudin shiga Naira dubu biyar (5,000). Amma mutane suka ki shiga. Ya rage kudin zuwa dubu Hudu (4,000) nan ma dai aka ki shiga, sai ya sake rage wa zuwa zuwa dubu biyu (2,000) a hakan ma aka ki shiga”.

To sai ya yi wata dabara, yace “duk mai son shiga ya zo ya shiga kyauta” ai nan da nan gidan ‘zoo’ din nan ya cika makil da mutane. Sai kawai ya je ya kunce Zaki. Ai kuwa jama’a suka yi ta gudun ceton rai, kowa yana kokarin fita. Sai yace “duk mai son fita, sai ya bada dubu Goma (10,000), haka aka yi ta biyan dubu goma-goma ana fita. To ka ga irin halin da masu son abu na kyauta yake jefa su.

Idan har za ka yi amfani da wayoyin nan na zamani, to ka kiyaye duk wani abu da aka ce na kyauta ne. Ko ka ga wani shafi an ce maka ana daukan ma’aikata, to ka yi kwakkwaran bincike kafin ka cika.

Abu muhimmi da mutum zai kiyaye shi ne, duk abin da aka ce maka ka saka email, password, lambar waya, lambar asusun ajiya, NIN number, da lambar BBN, to ka yi kwakkwaran bincike, bincike mai zurfi fa sosai, don wadanda suka daukar wa kansu wannan sana’a ta kutse a asusun ajiyar mutane da kutse a shafukan sada zumunta na mutane kullum suna kara fito da sabbin dabaru.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Za A Yi Jana’izar Tsohon Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Abdullahi Mahdi Da Yammacin Ranar Asabar

Next Post

Kai Wa Ofishoshinmu Hari Na Iya Kawo Cikas Ga Zaben 2023 – INEC

Related

Phishing
Rahotonni

2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

3 days ago
Tsadar Rayuwa: Yadda Al’umma Suka Yi Sallah Cikin Kunci
Rahotonni

Tsadar Rayuwa: Yadda Al’umma Suka Yi Sallah Cikin Kunci

4 days ago
Ana Fargabar Boko Haram Ta Kara Mamaye Wasu Kananan Hukumomi A Borno
Rahotonni

Ana Fargabar Boko Haram Ta Kara Mamaye Wasu Kananan Hukumomi A Borno

1 week ago
Kokarin Minista Tuggar Na Mayar Da Hijirar Masana Daga Nijeriya Zuwa Kasashen Waje Alhairi
Rahotonni

Kokarin Minista Tuggar Na Mayar Da Hijirar Masana Daga Nijeriya Zuwa Kasashen Waje Alhairi

1 week ago
Faduwar Jarrabawar JAMB Ta Tayar Da Bukatar Neman Sake Fasalin Hukumar
Rahotonni

Faduwar Jarrabawar JAMB Ta Tayar Da Bukatar Neman Sake Fasalin Hukumar

2 weeks ago
Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi
Rahotonni

Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi

2 months ago
Next Post
Kai Wa Ofishoshinmu Hari Na Iya Kawo Cikas Ga Zaben 2023 – INEC

Kai Wa Ofishoshinmu Hari Na Iya Kawo Cikas Ga Zaben 2023 - INEC

LABARAI MASU NASABA

Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Babban Taron MDD Kan Tekuna

Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Babban Taron MDD Kan Tekuna

June 10, 2025
Mutum 10 Sun Mutu Sakamakon Harbe-harbe A Makarantar Sakandire A Kasar Austriya

Mutum 10 Sun Mutu Sakamakon Harbe-harbe A Makarantar Sakandire A Kasar Austriya

June 10, 2025
Ba Mu Iya “Gina” Ayaba A Amurka

Ba Mu Iya “Gina” Ayaba A Amurka

June 10, 2025
Sarki Sanusi II Ya Yi Hawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda Na Haramta Hawan Sallah A Kano

Sarki Sanusi II Ya Yi Hawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda Na Haramta Hawan Sallah A Kano

June 10, 2025
Sojoji Sun Kashe Babban Kwamandan Boko Haram A Jihar Yobe

Sojoji Sun Kashe Babban Kwamandan Boko Haram A Jihar Yobe

June 10, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump: Yadda Sabuwar Dokar Hana Shiga Amurka Ta Fi Shafar Musulmai Da Afirka

June 10, 2025
Ƙungiyar G-5 Ta Ceto Nijeriya Daga Faɗa Wa Rikici — Wike

Ƙungiyar G-5 Ta Ceto Nijeriya Daga Faɗa Wa Rikici — Wike

June 10, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 51, 876 Sun Mika Wuya A Arewa Maso Gabas

Sojoji Sun Kashe Manyan ‘Yan Boko Haram A Gujba Da Malamfatori

June 10, 2025
Gwamnatin Borno Ta Nemi A Gaggauta Yashe Alo Dam Don Guje Wa Sabuwar Ambaliya

Gwamnatin Borno Ta Nemi A Gaggauta Yashe Alo Dam Don Guje Wa Sabuwar Ambaliya

June 10, 2025
Bam Ya Hallaka Masu Yawon Sallah A Sakkwato

Bam Ya Hallaka Masu Yawon Sallah A Sakkwato

June 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.