Sabon umarnin shugaban Amurka, Donald Trump, na hana matafiya daga ƙasashe daban-daban shiga Amurka ya fara aiki a ranar Litinin da misalin ƙarfe 5 na yamma.
Wannan mataki wani É“angare ne na manufofinsa na taÆ™aita Æ™auran jama’a zuwa Amurka, musamman daga Æ™asashen da yake kallon suna da barazana ga tsaron Æ™asar.
- Mataimakin Firaministan Sin Ya Gana Da Ministar Kudin Birtaniya
- Gwamnatin Bauchi Ta Buɗe Sabon Tsarin Neman Ƙirƙirar Sabbin Masarautu
Ƙasashe 12 ne aka haramta musu shiga Amurka gaba ɗaya, ciki har da Afghanistan, Myanmar, Chadi, Jamhuriyar Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Somalia, Sudan da Yemen.
Baya ga haka, an ɗora haramcin rabi da rabi kan ƙasashe bakwai: Burundi, Cuba, Laos, Saliyo, Togo, Trkmenistan da Venezuela.
Wannan umarni ya faru ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sukar manufofin Trump, musamman waɗanda ake kallon suna nuna bambanci ko wariya, musamman ga ƙasashen da yawancin Musulmai ne ko kuma ƙasashe masu tasowa a Afirka.
A wa’adinsa na farko a 2017, Trump ya kafa irin wannan haramci da ya shafi Æ™asashe bakwai ns Musulmai, wanda ya jawo gagarumar suka daga Æ™asashen duniya da Æ™ungiyoyin kare haƙƙin É—an Adam.
Masana harkokin tsaro da na diflomasiyya na ganin cewa wannan sabon mataki na iya ƙara tsamin dangantaka tsakanin Amurka da ƙasashen da abin ya shafa, musamman a lokacin da ake buƙatar haɗin kai tsakanin ƙasashen duniya wajen fuskantar manyan ƙalubale na tsaro da tattalin arziƙi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp