Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Raka da ke karamar hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato, inda suka kona gidaje da kayan abinci da dama kafin su tafi da wasu dabbobi da ba a bayyana adadinsu ba.
Leadership Hausa ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun kashe wata mata ‘yar shekara 120 da wasu mutane biyar.
- Sin Ta Sha Alwashin Kare Hakkokinta A Gabar Da Amurka Ta Sake Kakabawa Karin Kamfanonin Sin Takunkumi
- ‘Yansanda Sun Gano Wurin Da IPOB Ke Hada Bama-Bamai
Da aka tuntubi Hakimin yankin, Alhaji Sa’idu Wakili ta wayar tarho, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce duk da cewa ba a yi garkuwa da kowa ba, ‘yan bindigar sun kona kashi biyu bisa uku na gidaje da kayayyakin abinci tare da sace shanu.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da na jihohi da su kara zage damtse wajen magance matsalolin tsaro a yankin.
Hakimin ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su samar da gagarumin hanyoyin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.
Shugaban riko na karamar hukumar Tangaza, Alhaji Ibrahim Lawal Junju, tare da mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin tituna, Injiniya Mai Damma Tangaza, ya ziyarci al’ummar garin tare da jajanta wa mutanen kauyen sannan kuma ya yi alkawarin mika sakamakon bincikensa ga gwamnati domin taimakon wadanda abin ya shafa.
Jaridar Leadership Hausa ta rawaito cewa babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar ko kuma hukumomin tsaro har zuwa lokacin hada wannan rahoto.