Hukumar gudanarwa masarautar Kasar Saudiyya ta bai wa Nijeriya gurbin mahajjata 95,000 a hajjin shekara mai zuwa.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa sa Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON), ta fitar a shafinta na Intanet a ranar Laraba.
- Kakakin Majalisar Dokokin Taraba Ya Yi Murabus, Kizito Ya Maye Gurbinsa
- Babu Matakin Da Muka Dauka Kan Murabus Din Okupe – Kwamitin Yakin Zaben Peter Obi
Tuni dai hukumar ta fara karbar kudaden mahajjatan da ke shirin sauke farali a badi.
A hajjin bana dai an samu tsaiko, inda mahajjata da dama ba su samu damar zuwa Saudiyya ba sakamakon gaza samun jirgi da suka yi.
Sai dai daga baya NAHCON ta dora alhakin hakan a kanta, inda ta ce kamfanonin jiragen sama ne suka gaza cika alkawuran da suka dauka.
Hakan ne ya sanya hukumar jin dadin alhazan mayar wa da mutane da yawa kudaden da suka biya.
Ana dai sa ran Nijeriya za ta kammala shirye-shiryenta don gudun sake aukuwar abin da ya faru a hajjin bara.