Rundunar ‘Yansandan Jihar Kwara, ta cafke wani mutum, bisa zarginsa da hada kai da wasu mutane biyu wajen yin garkuwa da mahaifinsa tare da neman kudin fansa har Naira 2.5.
Mutumin dai, ya fada komar ‘yansanda ne a ranar 4 ga watan Janairu, 2023 inda jami’an sashen yaki da masu garkuwa da mutane suka kama shi a yankin Kambi da ke hanyar Ilorin zuwa Jebba.
- Sin Ta Yi Imani Da Karfin Jama’Ar Habasha Na Magance Harkokinsu Da Kansu
- Gidauniyar Abdulsamad Ta Bai Wa Hukumar NIS Kyautar 500m Don Inganta TsaroÂ
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce a lokacin da ake masa tambayoyi wanda ake zargin, ya amince cewa sun hada kai da wasu mutane biyu wajen yin garkuwa da mahaifin nasa.
“Jami’an sashen yaki da masu garkuwa da mutane sun cafke wani mutum a ranar 4 ga watan Janairu, 2023 a kusa da yankin Kambi da ke Ilorin.
“Lokacin da ake masa tambayoyi, ya bayyana cewa shi da wasu mutum biyu sun yi hadaka wajen garkuwa da mahaifinsa Bature Naigboho a yankin Igboho/Igbeti a Jihar Oyo tare da neman kudin fansa na Naira miliyan 2.5”.
Ya ce ana ci gaba da kokarin cafke sauran abokan cin burmin nasa, sannan kuma za mika lamarin zuwa Oyo.
Daga bisani ya ce Kwamishinan ‘yansandan jihar, ya sha alwashin tabbatar da tsaro da kare rayuka jama’a ganin yadda babban zaben 2023 da ke tafe.