‘Yan’uwana mata barkan mu da warhaka, barkan mu da sake haduwa a wannan makon. Da fatan kuna jin dadin abubuwan da muke tattaunawa a wannan shafi na Uwargida Sarautar Mata.
A wannan makon za mu yi ninkaya ne a cikin wani al’amari mai matukar amfani ta fuskar tsafta musamman abin da ya shafi ciki. Shi ne batun sanya kamfe wanda aka fi sani da pant. Na san da wuya a samu wata ‘ya mace da ba ta taba amfani da kamfai ba, don haka ba na bukatar dogon bayani game da ko mene shi. Domin karfafa amfani da kamfai, mun yo muku nazarin wasu daga cikin amfanoninsa.
Da farko amfani da kamfai yana hana kura shiga cikin al’aura wanda Ke haifar da warin gaba. Haka nan yana hana bushewar gaba wanda matsala ce da in ta faru tana haifar da kaikayin gaba.
Wani karin alfanun sa kuma shi ne yana kare mutuncin mace yayin da hadari ya same ta ko kuma al’adar ba-zata ya zo mata.
Sannan ga mace mai yawan fitar da farin ruwa a gabanta (discharge), sa kamfai yana rage yawan fitowar shi.
Saboda muhimmancin da sa kamfai yake da shi a wurin ‘ya mace, in akwai hali yana da kyau mace ta mallaki kamfai (panties) da yawa kamar kala 12 saboda ta dinga yawan canzawa saboda tsafta.
Haka Kuma ana so mace ta rika amfani da farin Pant a ko yaushe saboda yana saurin taimaka wa mace ta gane halin da gabanta ke ciki kamar ‘colour discharge’ dinta ko zuwan al’ada ba lokacin da ya saba zuwa ba wanda hakan zai sa ta dau mataki da wuri.
Mata a kula kar a dinga rabuwa da kamfai (Pant) sai lokacin bacci. Kuma yana da kyau mace har ‘ya’yanta ta koya musu hakan.