Nuna goyan bayan wani dan siyasa zai iya wayar da kan mai zabe a matakin kasa da jihohi na ‘yan takara wanda yakan kai ga cusa wa masu zabe ra’ayin wanda za su zaba da ya dace. Masu zabe da dama sukan kasance cikin rashin sani a lokacin da suka zo zaben dan takara saboda yadda ake bayyana masu ‘yan siyasa da kuma yadda tsarin siyasar take.
Bayani a kan rashin sani shi ne, yadda ake rarraba kan masu zabe. Wani bangare a kan wannan shi ne, dan takara da gangar sai ya je ya nemi wani fitaccen mutum ko sananne ko kuma wasu kungiyoyi sanannu su nuna goyon bayansa ta yadda za su rika amfani da shi wajen yakin neman zabe da suke yi.
Siyasar Nijeriya dai ta rarrabu ta bangaren addini da kabila da yanki da kuma jam’iyyun siyasa, wanda hakan ya sanya yake yi wa masu zabe matukar wahala kafin su nuna inda suka karkata. A saboda haka ne ya sanya masu zabe suke duba wanda aka nuna goyon bayansa da suka yi kamancececiya a daya daga cikin abun da suke so kuma suke bi.
Wadanda suke nuna goyon bayansu suna da matukar muhimmanci a kasa ana kuma girmama su sosai. A ko da yaushe ana jiran su nuna goyon bayansu ga wani dan takara ko wani tsari da ake yi, saboda ana ganin mutuncinsu da daukansu masu gaskiya ana kuma sonsu matuka. Su talakawan kasa a ko da yaushe suna jirann su ji wanda aka nuna goyon bayansa, kuma suna kushe duk wata kungiya ko wasu daidaikun mutane wadanda ba su cancanta ba, ko kuma ba sa ra’ayinsu.
Daga kudu, daya daga cikin dalilin nuna goyon bayan Atiku Abubakar da Chief Arthur Eze ya yi a wurin bikin kalankowa na Ofala tare da gwamna Charles Soludo da sauran sarakunan gargajiya.
Arthur Eze ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasar Nijeriya da ya cancanta a cikin kabilar Igbo shi ne Soludo. A halin yanzu duk wanda son ya inganta tattalin arzikin Nijeriya dole ya bi tsarin da Soludo ya yi. Ra’ayin Arthur Eze tsari ne na dogon lokaci ga wanda yake son ya amfanar da Nijeriya.
A wajensa da mutanensa, nuna goyon bayan wani zai iya haifar da matsala ga damar da Soludo ke da shi, wanda zai faru nan gaba. Shugabannin Igbo da mutanensa suna nan za su ci gaba da goyon bayan PDP.
Nuna goyon bayan da Yarima Eze ya yi ya kawo rarrabuwan kai na yadda kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi a karkashin tutar kudanci da shugabannin kungiyar yankin tsakiya idan aka koma watan Nuwamba. Kungiyar ta hada kungiyoyin Afenifere da PANDEF da shugabannin Middle Belt. Wani nuna goyon bayan wanda za a zaba wanda ya kara raba masu zabe shi ne, bangare na kungiyar Afenifere da suka ayyana cewa a zabi dansu, Bola Tinubu.
A daidai lokacin da ake rubuta wannan nazari, Tsohon Shugaban kasa , Obasanjo ya ayyana goyon bayansa ga Peter Obi ne. A cikin wani rubutun kundi da ya yi mai tsawon shafuka 6. Ya yi rubutu ne a kan matasan Nijeriya. Na sami wasikar da ya rubuta wanda ya fi karfin matasa masu zabe.
Hanyar sadarwar da aka yi amfani da shi ba a tsara shi ta yadda sakon zai kai gare su ba, kuma ma ‘yan kalilan ne daga cikinsu suke da hakurin da za su karanta rubutu da suka fi kalmomi 280.
A tunanin Obasanjo yana ganin kamar matasa ba a kyauta masu. Can sai na tuna da irin kiyayyar da ke tsakaninsa da ‘ya’yansa Gbenga da Iyabo. Iyabo ta taba rubuta wa mahaifinta wasika na rashin adalcinsa da san kai wanda ba ta jin dadinsa. Ko ma da mene ne wannan rudani na Obasanjo da kuma nuna goyan bayansa ga wani bai sami goyon kowani manyan tofaffin sojoji ba.
A ‘yan gaba-gaban Arewa kuwa, Yakubu Dogara da kungiyar Kiristocin Arewa an ji sun nuna goyon bayansu ga jam’iyyar PDP da ke yankinsu. Sai dai wanda ya fandare shi ne, Babachir Lawal wanda gwamnatin Buhari ta kora bisa almundahana na kwangilar cire ciyawa.
Ya yanke shawarar ya goyi bayan Peter Obi, bayan da Tinubu ya ki amsar bukatarsa na ba shi mukamin minista bayan an sami nasara. A wata hira da ya yi da sashin Hausa Muryar Amurka da gidan talabijin na Channels ya nuna rashin zamansa na nagartacce.
Kungiyar Izala ta JIBWIS wadanda ake dakon jiran jin wanda za su ayyana a goyi bayansa. Haka kuma Shugaban kungiyar, Abdullahi Bala Lau ya fara nuna inda ya karkata. Kamar shi ma Kabir Gombe. Dukkaninsu suna da kusan ra’ayi irin na Babachir, sai dai sun fi karkata ga Tinubu.
Mataimakin shugaban JIBWIS, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum ya nuna cewa Arewa ne ya kamata a sami shugaban kasa. Ba kamar Bala Lau da Kabir Gombe ba, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum yana ganin a rika bayyana wa mutane masu zabe sanin abubuwan da ya kamata su sani.
Nuna goyan bayan wani dan takara da ayyana shi yanzu aka fara. Zabe na karatowa za a rika jin ayyana goyon bayan ‘yan takara mabambanta. Kungiyar Kiristaoci na Nijeriya da manyan cocina har yanzu ba su ayyana goyon bayan dan takara daya tilo da za a zaba ba. Kungiyar Jame Ibori ba ta ayyana dan takararta ba, wanda masu zabe a yankin Kudu maso Kudu za su zaba.
Kungiyar Arewa ana jiran a ji dan takara daya tilo da za ta ce a goyawa baya, kamar yadda suka yi a lokacin da suka gayyaci ‘yan takarar shugaban kasa 6 a watan Oktoba 2022, a karkashin Gamayyar Kwamitin Arewa.
Ayyana dan takara da za su goyi baya babu shakka zai tabbatar da cewa zaben da za a yi za a yi a tsakanin yankuna uku na kasar nan ne. Kungiyoyin za su kasance tare da tsofaffin shugabannin kasa da wasu manyan sojoji masu murabus.
Wani abu na nuna goyon baya ga wani dan takara da masu zabe za su duba shi ne, wanda bijirarrun gwamnonin PDP 5 din nan da suka hada da Wike da Ortom da Ikpeazu da Ugwuanyi da Makinde. Duk da yake dai Wike ya ce zai sanar da matsayarsu na wanda za su zaba a watan Janairu. Jaridu sun ruwaito cewa sun yi taro da Tinubu a Landan, amma kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ya karyata wannan rahoton.
Ta tabbata cewa wadannan gwamnoni 5 ba su da alkibla wanda karara ta nuna cewa ba su ma san abun da suke so ba ko kuma zai amfane su. Haka kuma zawarcin da suke yi wa ‘yan takarar shugaban kasa 4 ya nuna cewa ba su san abun da suke so ba. Duk da yake a nan dimokuradiyya ne kuma abun da suka yi bai saba da tsarin doka ba.
Masu zabe wadanda suke bibiyan abubuwan da suke yi sun gane cewa ba mutane ba ne masu alkibla. Haka kuma duk tsayayyen dan siyasa da ya san abun da yake yi zai kaucewa kawance da ire-irensu. Za a Iya fahimtar dalilin da ya sa Atiku ya yi watsi da su.
A saboda haka, wanda suke ayyana wanda za a zaba su sani cewa masu zabe suna son su ji abun da suke fada ne, amma ba za su yi aiki da abun ba.
Za su iya daukan cewa masu zabe ba su san abun da suke yi ba, amma kuma mafi yawan masu zabe sukan kauce wa wadanda suka san ba su dace ba.