Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu, ya gargadi ‘yan Nijeriya kan zabar Atiku Abubakar, inda ya ce dan takarar na iya jefa miliyoyin mutane cikin yunwa.
Tinubu ya yi gargadin cewa Atiku zai iya sayar da duk kadarorin Nijeriya.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Tarwatsa Sansaninsu A Kaduna
- Gwamnatin Gombe Ta Nada Sabbin Shugabannin Rikon Kananan Hukumomi
A yayin da yake jawabi a yakin neman zabensa na shugaban kasa a Ilorin, a Jihar Kwara a ranar Talata, Tinubu ya ce zaben Atiku zai zama kuskure mafi girma da zai yi wuya a iya gyara shi.
Tinubu ya yi ikirarin cewa bayanai sun nuna cewa Atiku yana sha’awar zama shugaban Nijeriya ne kawai don ya wadata kansa da abokansa.
“Dan takarar jam’iyyar PDP ya shahara wajen sayar da duk wani abu da da Tarayyar Nijeriya a ta ke da su.
“Ba shi da wani buri face a ya siyar da dukiyar kasa sannan ya azurta kansa.
“Yana son sayar da damarku mai kyau, makarantu masu kyau, gidaje da rayuwa mai dadi. Burinsa shi ne ya sayar da komai ya kuma mayar da kadarorin jama’a. Yana so ya jefa ku cikin yunwa.”