Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya amince da zabtare kaso 35 cikin dari na kudin hayar shaguna a sabbin Kasuwannin zamani wanda gwamnatin jihar, wadanda ta bude don bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.
A sanarwar manema labaru mai dsuke da sa-hannun Darakta-Janar Kan hulda da yan Jarida, Kafafen yada labaru, Alhaji Mamman Mohammed, ya ce Gwamna Buni ya bayyana hakan biyo bayan mika rahoton farashin shagunan a matakin farko wanda kwamiti ya yi dangane da raba shaugunan ga yan kasuwa.
Har wala yau, Gwamnan ya bayyana cewa rage farashin shagunan ya zama dole saboda bai wa yan kasuwar cikakken goyon baya da kwarin gwiwa wajen gudanar da al’amarran kasuwancinsu cikin sauki a sabbin Kasuwannin.
Yayin da shagunan kasa masu ciki-biyu wadanda a tashin farko farashin su ya kama naira 468,000 a shekara, ya koma naira 304,200, masu ciki-daya naira 390,000 yanzu zasu biya naira 253,500 a shekara.
Haka kuma, shaguna masu fuska biyu a kasa kan naira 442,000 yanzu zasu biya naira 287,300, sauran shaguna masu ciki-biyu a kasa kan naira 390,000 an rage zuwa naira 253,500.
Shagunan saman bene masu ciki-biyu za a biya naira 253,500 maimakon naira 390,000, sai masu ciki-daya kuma naira 211,250, savanin 325,000 a shekara.
Shagunan saman bene masu fuskata biyu za a biya hayarsu naira 236,600, yayin da sauran suka kama naira 169,000. Sannan masu fuska daya farashin su ya koma naira 152,100 a shekara.
A hannu guda kuma, shagunan rukunin ‘B’ za a biya naira 185,900 maimakon naira 286,000, yayin da rukunin ‘C’ farashin su ya kama naira 211,250 sabanin 325,000 da farko, sai kuma shagunan sayar da nama za a biya haya kan naira 105,625 maimakon 162,500.
Yayin da shagunan sayar da kifi a Kasuwannin farashin ya koma naira 67,600 sabanin naira104,000, sauran sun koma naira 84,500, daga naira 130,000.
Bugu da kari kuma, manyan shagunan ajiya wanda za a biya hayar naira 650,000 sun koma naira 442,500. Wanda ya ce sabon farashin shagunan zai taimaka wajen inganta harkokin kasuwanci a Kasuwannin.