Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi barazanar sanyawa bankunan kasuwanci takunkumi da ba su fara raba sabbin takardun kudi ba.
Babban bankin ya sauya takardun kudi na Naira – N200, N500, da kuma N1,000 – sannan ya bayar da wa’adin ranar 31 ga watan Janairu domin daina karbar tsofaffin kudin a bankuna.
- Harkokin Diplomasiyya Na Shugaban Kasar Sin A Shekarar 2022
- Zaben 2023: Buhari Ya Kara Wa Sifeto Janar Na ‘Yansandan Nijeriya Wa’adin Aiki
Yayin da ya rage kasa da mako biyu wa’adin da ‘yan Nijeriya da dama ke korafin rashin samun sabbin takardun, mai kula da bankin koli na reshen Abeokuta a Jihar Ogun, Lanre Wahab, ya ce CBN ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sanyawa bankunan takunkumi kan rashin raba takardun ga kwastomomi.
Tun da fari dai mutane sun yu korafin cewar wa’adin da aka bayar ya yi kadan.
Amma CBN ya dage kai da fata kan wa’adin da ya kayyade na ranar 31 ga watan Janairu 2023.
CBN ya ce tuni ya buga adadi mai yawan gaske na kudin, wanda zai wadata ga masu amfani da kudaden.
Sai dai har yanzu jama’a na ci gaba da korafi kan yadda suke samun tsofaffin kudaden idan sun je banki ko injin cirar kudi na ATM.