A wannan makon zamu so jin ra’ayoyinku a kan wa’adin CBN na sauya tsofaffn takarar naira na ranar 31 ga watan Janairu 2023 musamman ganin har yanzu Bankuna na ci gaba da bayar da tsofaffin kudaden kuma Bankuna basusaya sabbin kudin a naurar ATM.
Abdul’aziz Mohammed
Hakikanin gaskiya wa’adin da CBN ya bayar ya yi kadan duba da karancin sabbin kudin a hanun al’umma. Daga karshe muna fatan CBN zai kara wa’adin zuwa wani lokaci saboda gujewa asarar da hakan zai haifar musamman ga mutanen kauyuka. Abdul’aziz Gombe, karamar hukumar Balanga.
Sulaiman Muhammad
Allah ya sa muda ce
Yusuf Muhammad Jalingo
Wannan doka na CBN ta yi kyau ta bangaren tattalin arziki amma sai dai kudin sun yi karanci a wajen mutane kuma lokaci sai kara matsowa yake yi, sai dai akwai abinda muke so CBN ya sani cewa kudi babu su a bankuna don ko yanzu kaje ATM ba zaka samu sabbin ba, duk dama akwai zargi na cewa shugabannin bankuna sun sayar ‘yan siyasa shi ne muke so muja hankalin CBN ya duba al’amarin.
Allah ya sa chanjin ya zama alkhairi ga ‘yan Nijeriya, Amiin.
Hamisu Ibrahim Yarima
To ni dai da farko banga wani amfani da sauya fasalin kudin nan ya yi ba.
Kuma gabaki daya ana so a takura tunanin talakan Nijeriya alhali babu takardun sababbain kudaden a kasa.
Duk lokacin da kaje banki to wannan tsofaffin kudin za su baka, Amma kuma a hakan CBN yake cewa za’a daina karbar tsofaffin kudaden.
Don haka ni a gani na afasa canja kudin nan, ko kuma aci gaba da amfani da sababbain da tsofaffin kawai. Ko kuma a kara wa’adin canja kudin.
Nuruddeen Muhammad Funtua
Muna kira ga Shugaban Kasa da shugaban bankin CBN da su taimaka su kara wa’adin saboda har yanzu Sabbin kudi basu wadata a bankunan Nijeriya ba, Allah dai ya kyauta
Abdullahi Duwale Mariri YaronMallam
Har ga Allah dai za a zalunci mutane sosai duba da cewa har yanzu kudin basu wadata ba a hannun jama’a ba
Jameel Moh’d
Tunda bani da kudi ni me zai shafe ni, mu rokon muke Allah ya bamu shugabanni adilai masu yi donn Allah
Hadiza Bello Hamza
Muna rokon CBN ya kara wa’adin don in ba haka ba al’umma da dama za su yi asarar duniyar su, saboda a halin yanzu kudaden basu isa ba. Mun gode da wannan dama da muke samu na bayyana ra’ayinmu a kan al’amurran kasar mu.
Buhari Abdullahi
Lallai sauya fasalin Nairar yana da matukar amfani amma wa’adin ya yi karanci, ya kamata a kara wa’adin ta yadda al’umma za su samu cikakken damar mayar da tsofaffin kudadensu zuwa bankuna kamar yadda aka tsara. Ina godiya, Allah ya taimaka.
Walida Musa
Ya kamata hukumar CBN su kara tunani don wannna wa’adin ya yi kadan