Masana’antar fina-finan Kannywood ta shiga alhinin matashi kuma jarumin barkwanci, Kamal Aboki wanda ya rasu a ranar Litinin a hatsarin mota.
Aboki ya rasu ne bayan wani hatsarin mota ya rutsa da shi a hanyar Maiduguri zuwa Kano.
- Dan Nijeriya Ya Shiga Hannu Kan Damfarar Bankuna A Amurka
- A Boye DSS Ta Ayyana Cafko Emefiele – Femi Falana
‘Yan uwa da abokan arziki da dama sun shiga bayyana ta’aziyyarsu a shafukan sada zumunta kan rasuwar matashin.
Am ruwaito cewar matashin jarumin barkwancin ya je Maiduguri ne inda ya halarci wani taro shi da abokinsa Dan Yarbawa da suke yin bidiyon barkwanci tare.
Aboki dai ya fara barkwanci a kafar Instagram, YouTube shekaru biyu da suka wuce, daga bisani ya fadada zuwa TikTok.
Matashin ya shahara wajen yin kiranye-kiranye, fadarkwa da sauransu a cikin bidiyo dinsa.
Tuni dai aka jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a unguwarsu da ke Hotoro a Jihar Kano.