Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad, ya hakikance kan cewa tazarcen da yake nema a kan kujerar gwamna na yi ne domin ya samu zarafi cigaba da gudanar da ayyukan sabunta jihar Bauchi da ma karasa wadanda ya faro a zangonsa na farko.
Ya ce, baya ga samar da ayyukan gina kasa, more rayuwa, samar da sauyi da romon dimokradiyya gwamnatinsa ta samu nasarar inganta tsaro, zaman lafiya tsakanin addinai, kabilu da yankuna mabanbanta a fadin jiha.
Bala na jawabi ne a fadojin Hakiman Sade da Darazo kafin daga bisani ya yi sansani a babban filin wasa dake cikin garin Darazo domin kaddamar da yakin neman zabe da rakiyar shugabannin jam’iyya da ‘yan takaran Majalisar jiha da na tarayya a ranar Lahadi.
Muhammad ya ce daga cikin ayyukan gwamnatinsa na farko-farko har da samar da katafariyar hanyar Sade zuwa Akuyam da a baya ake yiwa lakabi da gagara-badau kari bisa gyara wutar lantarki da aka shafe shekaru sama da sha biyar ba tare da ita ba.
Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na cigaba da samar da manyan ayyuka a mazabar Darazo baya ga wadanda ta samu nasarar kammalawa da suka hada da kwaskwarima wa fadar hakimin Darazo da takwaran sa na Sade da kuma sauran ayyukan da suka shafi makaranti, hanyoyi da asibitoci.