Rundunar sojin saman Nijeriya ta yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga da ba a tantance adadinsu ba a wasu hare-hare ta sama a yankin Tshohon Kabula da ke karamar hukumar Munya a Jihar Neja.
An tattaro cewa ‘yan bindigar da aka kashe su ne ragowar wadanda suka yi musayar wuta da jami’an tsaro na hadin gwiwa na jihar a unguwar Gwada da ke karamar hukumar Shiroro a yammacin Lahadin da ta gabata, inda wasu daga cikinsu suka gamu da ajalinsu.
- Na’urar Lantarki Ta Kawo Cikas Yayin Gangamin Yakin Zaben Tinubu A Bauchi
- Makamashi Mai Tsafta Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Isasshen Makamashi A Sin
Wata majiya daga yankin ta ce, an kai farmakin da jiragen yakin sojin sama kan wurin da ‘yan bindigar suka kai da misalin karfe 9:00 na safe, inda aka kashe da dama, yayin da wasu suka tsere da raunuka daban-daban.
Kafin kai harin ta sama, Leadership Hausa ta samu labarin cewa a yammacin ranar Lahadi ne rundunar hadin guiwar jami’an tsaro ta jihar ta yi artabu da ‘yan bindigar a kan hanyar Gwada a kan hanyarsu ta zuwa kauyen Egwa inda suka dauki lokaci suna artabu.
An tattaro cewa an dauki matakin karfafa rundunar tsaro ta hadin gwiwa daga yankin Erena domin fatattakarsu duk da cewa jami’an tsaro uku sun samu raunuka a yayin musayar wutar.
Kafin harin da yammacin ranar Lahadi, an girke jami’an tsaro don dakile kai hari a yankin.
Idan dai za a iya tunawa kwanaki biyu da suka gabata ‘yan bindiga sun kashe kansila mai wakiltar mazabar Allawa, Mallam Sale Yakubu yayin da mataimakinsa ya tsere.
Sai dai kokarin jin ta bakin gwamnatin jihar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ci tura har zuwa lokacin hada rahoton.