• English
  • Business News
Sunday, August 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping Ya Gabatar Da Sakon Bidiyo Ga Taron Koli Karo Na 7 Na Kungiyar Kasashen Latin Amurka Da Caribbean

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Xi Jinping Ya Gabatar Da Sakon Bidiyo Ga Taron Koli Karo Na 7 Na Kungiyar Kasashen Latin Amurka Da Caribbean
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A jiya Talata 24 ga watan nan ne aka gudanar da taron koli na bakwai, na kungiyar kasashen Latin Amurka da Caribbean, a birnin Buenos Aires, fadar mulkin kasar Argentina.

Bisa goron gayyatar da shugaban kasar Argentina, kuma mai rike da shugabancin kungiyar a wannan karo Alberto Fernández ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi ta bidiyo a gun taron.

Cikin jawabin na sa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasashen yankin Latin Amurka da Caribbean, na kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin, don inganta raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” mai inganci, da ba da goyon baya da shiga ayyukan shawarar ci gaban duniya, da ta kiyaye tsaron duniya.

Baya ga haka, Xi Jinping ya jaddada cewa, a halin yanzu, duniya ta shiga wani sabon yanayi na tinkarar tashin hankali da sauye-sauye, kuma ta hanyar karfafa hadin kai ne kadai za a iya tinkarar kalubale, tare da shawo kan matsaloli tare.

Ya kara da cewa, kasarsa tana son yin aiki tare da kasashen Latin Amurka da Caribbean, don ci gaba da inganta zaman lafiya da bunkasuwar duniya, da sa kaimi ga gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga bil’adama, da samar da makoma mai kyau tare. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

Labarai Masu Nasaba

Babban Bankin Sin Ya Yi Alkawarin Ba Da Goyon Baya Ga Kirkire-Kirkire Da Sayayya

Fim Na Kisan Kiyashin Nanjing Ya Mamaye Kasuwar Fina-Finan Sin Bisa Samun Kudin Shiga Yuan Biliyan Daya

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Ruwa Abokin Aiki: Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Samar Da Alfanu Ga Rayuwar Al’ummar Afirka

Next Post

An Fara Aiki Da Sashen Farko Na Layin Dogon Da Sin Ta Gina A Lagos 

Related

Babban Bankin Sin Ya Yi Alkawarin Ba Da Goyon Baya Ga Kirkire-Kirkire Da Sayayya
Daga Birnin Sin

Babban Bankin Sin Ya Yi Alkawarin Ba Da Goyon Baya Ga Kirkire-Kirkire Da Sayayya

20 hours ago
Fim Na Kisan Kiyashin Nanjing Ya Mamaye Kasuwar Fina-Finan Sin Bisa Samun Kudin Shiga Yuan Biliyan Daya
Daga Birnin Sin

Fim Na Kisan Kiyashin Nanjing Ya Mamaye Kasuwar Fina-Finan Sin Bisa Samun Kudin Shiga Yuan Biliyan Daya

21 hours ago
Babban Jami’in MDD: Kokarin Sin A Fannin Samun Ci Gaba Mai Dorewa Na Da Matukar Alfanu Ga Yanayin Duniya
Daga Birnin Sin

Babban Jami’in MDD: Kokarin Sin A Fannin Samun Ci Gaba Mai Dorewa Na Da Matukar Alfanu Ga Yanayin Duniya

22 hours ago
An Dawo Da Wutar Lantarki A Dukkan Kauyukan Da Aka Tafka Ruwa Da Iska A Beijing
Daga Birnin Sin

An Dawo Da Wutar Lantarki A Dukkan Kauyukan Da Aka Tafka Ruwa Da Iska A Beijing

23 hours ago
Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine

2 days ago
Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu

2 days ago
Next Post
An Fara Aiki Da Sashen Farko Na Layin Dogon Da Sin Ta Gina A Lagos 

An Fara Aiki Da Sashen Farko Na Layin Dogon Da Sin Ta Gina A Lagos 

LABARAI MASU NASABA

Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM

ADC Ta Yi Allah-wadai Da Rufe Gidan Rediyon Badeggi FM A Neja

August 3, 2025
Gwamnatin Katsina Ta Gabatar Da Matsayarta A Taron Jin Ra’ayiyin Jama’a

Gwamnatin Katsina Ta Gabatar Da Matsayarta A Taron Jin Ra’ayiyin Jama’a

August 3, 2025
Borno Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijira 5,000 Kafin Damuna Ta Kare

Borno Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijira 5,000 Kafin Damuna Ta Kare

August 3, 2025
Samun Kuɗi Ya Fi Samun Ɗaukaka Wahala A Kannywood -Baba Sadiƙ

Samun Kuɗi Ya Fi Samun Ɗaukaka Wahala A Kannywood -Baba Sadiƙ

August 3, 2025
Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM

Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM

August 3, 2025
Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

August 3, 2025
Ban Yi Danasanin Shiga Harkar Fim Ba – Baba Ƙarami

Ban Yi Danasanin Shiga Harkar Fim Ba – Baba Ƙarami

August 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji

Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji

August 3, 2025
Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

August 3, 2025
Sanata Buba Ya ƙaryata Jita-jitar Cewa Majalisa Ta Amince da ƙirƙiro Sabbin Jihohi 12

Sanata Buba Ya ƙaryata Jita-jitar Cewa Majalisa Ta Amince da ƙirƙiro Sabbin Jihohi 12

August 2, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.