Wanda ya dau nauyi kuma ya shirya Fim din Manyan Mata, da akai wa lakabi da Premier Fim Series, Manyan Mata, Abdurahman Muhammad, wanda akafi dani da Abdul`amat Mai-kwashewa, ya bayana cewa duk fina-finansa ya na yi ne bisa la’akari da kyawawan al’adunmu da addininmu ta yadda ko da zaka kalla da iyalai, da ‘ya’ya da sirikai, mai kallon fim ba zai kunyata ba wannan shi ne tsarin da nayi a wannan fim na Manyan Mata, wanda za a fara haskawa gobe Asabar in Allah ya kaimu.
Mashiryin fim din ya bayana hake ne a lokacin da ya ke hira da wakilin Jaridar LEADERSHIP HAUSA, jim kadan da fitowa daga ‘Film House Cinema’, Ado Bayero Mall, inda aka fara nuna fim din Manyan Mata, a matsayin gwaji inda aka gayyaci manyan masu shirya fim na kasa da daraktocin finafina da jariman fina-finai har ma da shugabannin kungiyoyin shirya fina-finai na kasa, MAFORM wanda aka yi a ranar Asabar da ta gabata a birnin Kano.
Har ila yau ya ce wannan fim ya kunshi fadakarwa ce a kan illar shaye-shayen miyagun kwayoyi, tallace tallace, gallazawa mata, ko bautar dasu alhalin aure aka yi ba baiwa bace haka kuma akwai fadakarwa kan illar fade barace barace, da sunan almajirci, ilimin mata, bangar siyasa, da halin da yan gudun hijira, da dai sauransu kuma wannan fim na ‘Manyan Mata’ an shirya ne kashi 70 ne da kashi 30 a kan kirkiranran labari da labari na gaskiya, kuma da alamu fim din samu karbuwa, duk da babu wani kalo bale da na fuskanta wannan aiki amma muna sauraran shawarwari da zarar anfara haskaka fim dina gobe inda ya kara da cewa wannan fim na Manyan Mata yana son ya canza rayuwar al’umma daga ba dai dai ba zuwa dai dai kamar yadda ya ke alfahari da fim din Salma da ya yi wanda ya canza shigar mata ta kammala a bukukuwan sallar da tazo bayan nuna fin din Salma, wanda yanaji a ransa ya yi wani akin a daukaka addini da al`ada a cewar Mai-Kwashewa.
Shi ma daraktan fim din mai suna Sadik Abubakar, wanda aka fi sani da M Mafiya, ya ce wannan fim yana da dugon zango 26 kuma ya kunshi komai da komai na rayuwar al`umma don fadakarwa kuma fim din an yi la’akari da al’ada da addini, kuma ni dama inayin fim ne wanda ko bayan rai na fim din ba zai zama matsala ga zuriya ta ba, kuma inaso daukacin masu ruwa da tsaki su rika yin fina finai irin wadanan ta yadda wasu ba za su hau mambarin su zage ni ba domun muna fina finai masu kyau amma ba a gani amma da munyi kuskure sai kaji wasu suna zaginmu a cewar N Mafiya, wanda shi ne daraktan fim din Manyan Mata.
A karshe shi ma daya daga cikin manyan baki da suka kalli fim din a karon farko Dakta Ahmad Sarari, shugaban kungiyar masu shirya fina finai ta kasa MAFORM ya ce wannan fim ya yi kuma ya zo da sabon salon a kayatarwa kuma lallai gurin da ake galazawa mata a wannan fim abu mai daukar hankali sosai dama sauran sakonin da ke cikin wannan fim na Manyan Mata premier Fim Series, Manyan Mata.
Wakilinmu wanda guda ne daga cikin wadanda suka kalli wannan fim a karo na farko da ak nuna shi, ya ce nuna wannan fim na gwaji ya samu halatar irinsu Alhaji Ado Gidan Dabino, Alhaji Alkanawi, Ibrahim Mandawari, da dai sauran futattu masu ruwa a harkar fina finai na wasan kwaikwayo a matakin jahar kano da kasa baki daya.