Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilan da ya sa gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ke sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan batun canjin kudi.
Ya mayar da martani ne biyo bayan kalaman gwamnan game da zaben shugaban kasa da ake shirin shiga.
- Boko Haram Ta Hallaka Malaman Makaranta Sama Da 2000 A Shekara 8
- Gwamnatin Neja Ta Bayar Umarnin Kama Duk Wanda Ya Ki Karbar Tsofaffin Kudi
A wata hira da ya yi da a Abuja a ranar Talata.
“Ya kamata Buhari ya jira karin wasu kalaman sukar daga Elrufai saboda dalilai uku.
“Biyayyar da El-Rufai ke yi wa Buhari ta kare. Ya samu duk abin da yake so a wajen Buhari, yanzu Buhari ba shi da amfani a wajensa.
“Karfin Buhari da tasirinsa a siyasa ya zo karshe; El-Rufai ya koma tsagin Tinubu.
“El-Rufai yana yi wa Buhari hidima ne don biyan bukatar kansa.
“Buhari ya watsar da dukkan abokansa nagari da suka yi masa hidima kuma suka sadaukar da kansu tsawon shekaru a Kaduna saboda kaunarsa ga El-Rufai. Mun gargade shi a kan El-Rufai amma ya yi biris; lokaci ya yi da Buhari zai san cewa abin da ya girka ya kwashe.
“Ban taba yarda cewa El-Rufai na son Buhari ba, ban taba yarda El-Rufai ya taba yi wa Buhari biyayya ba, na san duk wani abu da ya faru da shi, kuma na san cewa wannan rana za ta zo, El-Rufai ya ce yana son Buhari, kawai dai ya kwantar da kai ne domin ya samu duk abin da yake so a wurin Buhari kuma yanzu Buhari ba shi da wani amfani a gare shi.
“El-Rufa’i ya kwashe shekaru takwas yana yabon Buhari kuma Buhari ya kwashe shekaru takwas yana yabon El-Rufai duk lokacin da ya zo Kaduna; Buhari ya aminta ya ajiye kunama a kusa da shi.
“Ya kamata Tinubu ya kula da El-Rufai. El-Rufai ya fi son Amaechi ba Tinubu ba. Wakilan APC na Kaduna Amaechi suka zaba ba Tinubu ba.
“Ya kamata Tinubu ya yi taka-tsan-tsan don kada El-Rufai ya yi masa abin da ya yi wa Buhari.
“El-Rufai bai taba son talaka ba kuma ba zai taba son shi ba,” in ji shi.