A yayin da ake ci gaba da fuskantar tsaiko wajen tura kudi ta intanet da kuma amfani da na’urar cirar kudii ta PoS, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya musanta bayanan da ake yadawa cewar ya bayar da umarnin katse hanyoyin tura kudi ta intanet a lokacin zaben da za a yi a ranar Asabar.
Labarin ya jefa fargaba a zukatan mutane har ta kai mutane sun fara rige-rigen zuwa kasuwanni domin tanadar abubuwan bukata kamar abinci da man fetur domin ajiye su a gida har zuwa lokacin da za a kammala zabe.
- Zabe: ‘Yan Siyasa Sun Boye Tsofaffin Kudi Sama Da Biliyan 500 Ba Su Mayar CBN Ba – Bawa
- INEC Ta Haramtawa Masu Zabe Amfani Da Wayar Salula Yayin Kada Kuri’a A Rumfar Zabe
Labarin da ya karade ko ina musamman a kafar WhatsApp.
A ranar Laraba ne dai CBN ya karyata rahotannin da ake ta yadawa ba tare da yin karin haske kan batun ba.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, CBN ya ce babu gaskiya a labarin katse Intanet kuma ba daga wurinsa sanarwar ta fito ba.
Canjin kudi a Nijeriya dai ya janyo cece-kuce a bangarori da dama tun bayan fara aiwatar da tsarin a Disambar 2022.
Lamarin dai ya sa an yi ta samun bayanai na karya kan tsarin sakamakon rashin fitowar Babban Bankin Nijeriya na kin yi wa mutane bayani dalla-dalla game da manufarsa ta bijiro da shi.
Rarrabuwar kan da aka samu kan batun saka wa’adin mayar da tsofaffin takardun kudi zuwa ga batun ci gaba da amfani da su da kuma bayanan da aka rika samu daga bankuna sun jefa jama’a cikin fargaba da kuma rashin sanin alkiblar da za su bi.
Daga cikin irin wadannan bayanai masu janyo rudani da aka yi ta yadawa a baya-bayan nan akwai wanda ke cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi na N500 da N1000 har zuwa 1 ga watan Mayun 2023.
Sai dai kotun kolin da ke sauraren shari’ar da gwamnonin APC suka shigar ta sake dage zaman har zuwa ranar 1 ga watan Maris mai zuwa.