An shiga rudani game da takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyyar NNPP kasancewar bayanai na nuna cewar har yanzu sunan Sanata Malam Ibrahim Shekarau ne a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Wannan na zuwa ne duk da irin kokarin da bangaren NNPP suka yi na nusar da INEC tare da rubuta musu takardar cewa sun sauya sunan Shekarau da na Sanata Rufa’i Sani Hanga.
- Zabe: ‘Yan Siyasa Sun Boye Tsofaffin Kudi Sama Da Biliyan 500 Ba Su Mayar CBN Ba – Bawa
- Dan Majalisa Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP A Jigawa
A tattaunawarsa da BBC Hausa, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce shi da kansa ya rubuta wa INEC cewa a sauya sunansa saboda ya bar jam’iyyar.
Amma a cewar INEC lokacin sauya sunan dan takara ya wuce, sai dai, idan dan takara ne ya rasu.
Ya ce tuni ya bar jam’iyyar NNPP kuma ba ita yake wakilta ba, inda ya ce ko da ya ci zabe ba a cikinta yake ba.
Shekarau ya kuma ce ya kira wanda yake takarar kujerar ta Sanata a jam’iyyar NNPP, inda ya ce masa ya dakatar da yakin neman zabe saboda ba sunan shi ne a jerin sunayen da INEC ta fitar ba.
NNPP ta ce ta rubuta wa INEC a rubuce sunan dan takarar da ya maye gurbin Sanata Shekarau.