Jami’an ‘yan sanda a Jihar Zamfara sun kashe wani dan bindiga tare da kwato bindiga kirar AK 47 da alburusai 18 a wani artabu da suka yi a kauyukan Saran Gamawa da Anguwar Mata da ke Karamar Hukumar Gummi a Jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya fitar a Gusau ranar a Litinin.
- Za A Shafe Shekaru Kafin A Kawo Karshen Yakin Ukraine Da Rasha —NATO
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Coci, Sun Kashe Mutane 3 A Kaduna
“A ranar 19 ga Yuni, 2022, jami’an ‘yan sandan da aka tura ta hanyar Gummi/Bukkuyum, sun samu kiran gaggawa cewa, ‘yan ta’adda dauke da makamai a kan babura sun kai farmaki Saran Gamawa da kauyukan Unguwar Mata da ke makwabtaka da su da nufin sace mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
“Rundunar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar ‘yan banga na kauyukan da lamarin ya shafa, sun hada karfi da karfe tare wajen yakar ‘yan ta’addan a wani kazamin artabu da aka dauki tsawon sa’o’i ana yi.
“Sakamakon haka, daya daga cikin ‘yan ta’addan ya samu munanan raunuka, an samu bindiga kirar Ak 47 a wajen dan bindigar, yayin da wasu da dama suka tsere cikin dajin da raunukan harbin bindiga daban-daban,” in ji Shehu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, ya yaba da jajircewar da ‘yan sandan suka yi, ya kuma bukace su da kada su yi kasa a gwiwa wajen ganin rundunar ta kare rayuka da dukiyoyin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a jihar.
Elkanah ya kuma umarci Kwamandan yankin Anka da DPO da ke makwabtaka da su tura tawagar hadin gwiwa don ci gaba da sintiri don dakile ci gaba da kai hare-hare a kan al’ummomin da ke yankunan.
Ya ce rundunar ta kuma tura domin ceto mutanen biyu da maharan suka yi garkuwa da su kafin isowar ‘yan sanda.
“Yayin da yake tabbatar da kudurin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi a jihar, ya yi kira ga jama’a da su ba ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro hadin kai a kokarin kawar da ‘yan bindiga a jihar,” in ji kakakin.