A dukkan fadin Afirka, Nijeriya ita ce kan gaba wajen noman Karas, inda aka kiyasata cewa, a kasar ana noman Karas da ya kai tan 225,000 a duk shekara.
Wannan adadin ya kai kashi 37.5 daga cikin dari, inda kuma ake samun ribar da ta kai dala miliyan 720, wanda hakan ke nuna cewa, wannan wata babbar hanya ce, ta kara samar da kudin shiga da kuma kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
Sai dai, wani babban abin takaici shi ne, duk da karfin da kasar nan ke da shi wajen nomansa, wasu daga cikin manomansa na garin Jos, cikin jihar Filato sun bayyana cewa, nomansa bai da wuya kamar noman sauran kayan lambu.
Daya daga cikin manomansa a yankin Mista Ali a karamar hukumar Jos ta arewa,
Murtala Hudu ya bayyana cewa, ana samun riba mai yawa a nomansa kuma ba a bukatar sai an zuba jari mai yawa.
Ya ce, ba a bukatar sai manominsa ya zuba takin zamani mai yawa, sabanin a noman dankali ko Kabeji da sauran kayan lambu.
Ya kara da cewa, noman Karas na sa manoma su kara samun karuwa sosai, musamman idan suka noma shi yadda ya kamata, sannan kuma ya kara da cewa, momaninsa zai iya kashe naira 50,000 a wajen nomansa, inda kuma idan ya debe shi, zai iya samun ribar da ta kai ta naira 300,000 ko kuma naira 400,000.
Shi ma wani manomin sa mai suna Abdulkadir Danke ya bayyana cewa, noman sa bai da wata wahala sabanin sauran kayan lambu, inda ya kara da cewa, ana samun riba mai yawa a nomansa natukar manominsa ya dukkan ka’idojin shukarsa.
A cewarsu, akwai wani lokacin da farashin sa a kasuwa ke sauka, musamman idan manomansa, sun kai shi kasuwa da yawa, inda suka kara da cewa, akasari hakan na faruwa ne saboda karancin wajen da za su adana shi.
Sun bayyana cewa, wani lokacin dilolin na sayen daukacin kadadar da aka noma shi akan naira 80,000, inda suka yi nuni da cewa, a yar da shi a kan wannan farashin tabka babbar asara ce.
Sun kara da cewa, zai yi wuya su iya magance wannan matsalar kan yadda kasuwarsa ke kasance wa, inda suka sanar da cewa, kowanne manominsa, dole ne ya kwana da sanin cewa, zai iya yin asara a fannin na bonanza da kuma sanin ina ne kasuwarsa za ta karkata.
Sun kuma ce, tsadarsa na fara wa ne daga watan Afirilu zuwa watan Yuli kafin damina ta kankama sosai.
Shugaban kungiyar masu sayar da Karas reshen Jos Alhaji Tanimu Isa ya bayyana cewa, shiga cikin fannin noman sa a yankin da mutane suka yi da dama, hakan ya janyo faduwar darajar noman sa a yankin.
A cewarsa, sabanin a baya, a garin Jos ne aka fi yin nomansa, inda kuma a yanzu jihar Bauchi da Kano suke nomansa.