A ranakun 4 da 5 ga watan Maris na bana, za a gudanar da tarukan kasa guda biyu a nan kasar Sin, wato cikakken zama karo na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na jama’ar kasar Sin karo na 14, da kuma cikakken zama karo na farko na babban taron wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 bi da bi.
Ajandar babban taron wakilan jama’ar kasar Sin na wannan karo, shi ne duba rahoto game da yadda gwamnatin kasar Sin ta sauke nauyin dake biya wuyanta a bara, da aikin da za ta yi a bana. Sannan wakilan jama’a za su duba rahoto kan yadda aka aiwatar da shirin raya tattalin arzikin kasa da ci gaban jama’a na shekarar 2022 da daftarin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar kasa na shekarar 2023, da daftarin tattalin arzikin kasa na shekarar 2023, da shirin ci gaban zamantakewa, da kuma nazarin tsarin tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al’umma, da duba rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’a, duba rahoton aiki na kotun koli, duba rahoton aiki na majalisar koli ta jama’a, zabe da kuma nada sabbin jami’an hukumomin gwamnatin kasar Sin, kamar su firaministan gwamnatin kasar, da mataimakansa da ministocin gwamnati, da dai sauransu.
Ajandar taron kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa na jama’ar kasar Sin shi ne saurara da duba rahoton ayyukan zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin, da rahoton ayyukan shawarwari, dubawa da zartas da gyaran kundin sauraran shawarwari na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin, ya kuma zabi shugaba da mataimakansa da babban sakatare da mambobin zaunanen kwamitin na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na jama’ar kasar Sin karo na 14 da dai sauransu.
Akwai sabbin abubuwa da yawa a cikin tarukan kasa guda biyu na wannan karo, wanda ke jan hankalin jama’a a duk fadin kasar. A siyasance, sabbin wakilan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da mambobin kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa na jama’ar kasar Sin za su halarci tarukan biyu. A lokacin, wakilai da ’yan kwamiti daga wuraren kasar daban daban za su gudanar da ayyukansu, kana za su tuntubi juna da ba da shawarwarinsu. A sa’i daya kuma, yayin da aka fitar da jerin sunayen “manyan shugabanni” da tawagogin jagoranci na cibiyoyi daban daban, fagen siyasar kasar Sin zai kammala mika mulki tare da kafa wani sabon layi. Kamar yadda aka saba, sabon firaministan kasar Sin da mataimakin firaministan majalisar gudanarwar kasar Sin, za su fito fili don ganawa da ‘yan jaridun kasar Sin da na kasashen waje. A madadin sabuwar gwamnatin tsakiya, sabon firaministan zai amsa tambayoyi daga manema labarai, da gabatar da manufofin da kuma mayar da martani ga tsammanin jama’a.
Ta fuskar tattalin arziki, yadda za a tsara ingantaccen ci gaba a cikin rahoton ayyukan gwamnati na wannan shekara, musamman ma abin da aka sa a gaba ga tattalin arzikin kasar a shekarar 2023, ya cancanci a ci gaba da kula da su. A game da rayuwar jama’a, sabon kwamitin wakilan zai tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arzikin kasa da rayuwar jama’a, da tabbatar da burin jama’a na samun ingantacciyar rayuwa a hakika, da rubuta wani sabon labari game da dimokradiyyar kasar Sin. A fannin yin gyare gyare da bude kofa ga waje, bana shekara ce ta cika shekaraku 45 da gudanar da manufar yin gyare gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje ta kasar Sin, kana sabbin matakan gyare gyare da bude kofa ga kasashen waje da kasar Sin ta dauka sun jawo hankalin duniya baki daya. Wadanne irin matakan bude ido ne majalisar wakilan jama’ar kasar za ta dauka a bana cike da fata?
Ta fuskar diflomasiyya, shugaban kasar Philippines, da shugaban Turkmenistan, da firaministan Kambodia, da shugaban kasar Iran sun ziyarci kasar Sin cikin nasara, dangantakar diflomasiyya tsakanin shugabannin kasa da kasa ta fara shiga wani sabon matsayi a farkon wannan shekara. Shekarar bana ta zo daidai da cika shekaru 10 da gudanar da shawarar “Ziri daya da hanya daya”, kuma yadda kasar Sin za ta ba da labarin hadin gwiwa kan “berin raya kasa” da “hanyar farin ciki” a harkokin diflomasiyyar cikin gida shi ma zai jawo hankalin jama’a. Bugu da kari, wannan shekara ita ce karon farko da sabon ministan harkokin wajen kasar Sin zai bayyana a tarukan biyu bayan kama aiki. Ta hanyar lura da taron manema labarai na ministan harkokin wajen kasar, kasashen waje na iya samun dan karamin ilimi da karin haske kan sabbin hanyoyin da ake bi na diflomasiyyar manyan kasashe.
Yadda tsarin dimokuradiyya irin na kasar Sin ke aiki yadda ya kamata, da tarukan kasa guda biyu, za su ba da wani kyakkyawan misali ga kasashen waje. A cikin tsarin kasar Sin, tarukan kasa guda biyu na kasar Sin sun kasance muhimman abubuwa wajen aiwatar da tsarin dimokuradiyyar jama’a a dukkan matakai, kuma wannan shi ne cikakken tsarin dimokuradiyyar jama’a a dukkan matakai.
Tsarin dimokuradiyyar jama’a a dukkan matakai wani takaitaccen bayani ne na tsarin dimokuradiyya na jama’ar kasar Sin, tsarin dimokuradiyyar jama’a a dukkan matakai yana bin ka’ida ta tsakiya da jama’a ta farko, kuma wani salo ne na siyasa da dukkan jama’a za su iya shiga cikinta. Babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, ya zama wajibi a samar da cikakken tsari na hukumomi da gudanar da ayyukan hadin gwiwa, domin tabbatar da cewa jama’a na da ‘yancin shiga ana damawa da su, da ci gaba da zurfafa harkokin siyasa na yau da kullum.
Dimokuradiyyar “jama’a” ita ma wata muhimmiyar alama ce da ke banbance dimokuradiyyar gurguzu mai tsarin musamman ta kasar Sin da dimokuradiyya irin ta nahiya Turai. Duk da cewa dimokuradiyya irin ta kasashen yamma ita ma tana tallata “ ‘yancin jama’a”, a aikace, da wuya a iya tabbatar da ‘yancin siyasa na mutane masu karamin karfi, abu ne mai wahala a mayar da ra’ayoyin dake shafar moriyarsu zuwa manufofi na hakika, ko da ya zama manufa, yana da wuya a aiwatar da shi yadda ya kamata.
A shekarar 2019, babban sakatare Xi Jinping ya ba da shawara a karon farko cewa, “tsarin demokiradiya da ya shafi al’umma baki daya”. A cikin daftarin gyare gyaren da aka yi wa dokar dabi’ar majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da ka’idojin gudanarwa na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da aka zartar a watan Maris na shekarar 2021, an rubuta “tsarin demokiradiya da ya shafi al’umma baki daya” a fili.
A cikin watan Oktoba na shekarar 2022, rahoton babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 ya bayyana cewa,bunkasa “tsarin demokiradiya da ya shafi al’umma baki daya”, wani muhimmin abu ne da yake kunshe cikin muhimman bukatu wajen zamanantar da kasar Sin, ya kuma jaddada cewa, tsarin dimokuradiyyar jama’a a dukkan matakai shi ne muhimmiyyar siffa ta siyasar dimokuradiyyar gurguzu, kuma gabatar da wasu bukatu wajen bunkasa dimokuradiyyar jama’a a dukkan matakai da kuma tabbatar da cewa jama’a su ne masu mulkin kasar nan. Wannan yana da ma’ana mai girma ga sabon zamani da sabuwar tafiya don kara yin amfani da moriyar tsarin siyasar gurguzu na kasar Sin, da gina kasa mai ra’ayin gurguzu ta zamani baki daya, da sa kaimi ga ci gaban babban farfadowar al’ummar kasar Sin.
Don bunkasa dimokuradiyyar jama’a a dukkan matakai, kamata ya yi a ba da cikakken dama ga muhimmiyar rawar da tsarin majalisar wakilan jama’a ke takawa, muna bukatar yin aiki mai kyau a cikin wadannan bangarori. Na farko shi ne tabbatar da shugabancin jam’iyyar, jama’a su ne masu mulkin kasar nan, da bin doka da oda, a ci gaba da fadada shigar jama’a a siyasance, da tabbatar da cewa jama’a sun samu ‘yancin walwala da dama kamar yadda doka ta tanada.
Na biyu shi ne aiwatar da cibiyoyi da hanyoyin da suka dace na kundin tsarin mulki da dokoki kan dimokuradiyya, da kuma amfani da tsare-tsare na kimiyya da inganci don tabbatar da cewa an aiwatar da ka’idojin da kundin tsarin mulki da dokoki suka kafa da kuma kiyaye martabar dokokin kasar.
Na uku shi ne, kyautata tsarin shari’ar gurguzu mai siffar kasar Sin, da ta taka cikakken rawa wajen jagorancin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da zaunannen kwamitinta kan ayyukan kafa dokoki, da kiyaye doka ga jama’a, da dogara ga jama’a, da amfanar da jama’a, da kuma kare jama’a, da kuma kara inganta dokoki na kimiyya da dimokuradiyya don inganta ci gaba bisa dokoki masu kyau.
Na hudu shi ne karfafa sa ido kan majalissar wakilan jama’a don tabbatar da aiwatar da dokoki da ka’idoji yadda ya kamata.
Na biyar shi ne ba da cikakken dama ga aikin majalisar wakilan jama’a, kulla alaka ta kut da kut da jama’a, sauraron ra’ayoyi da shawarwarin jama’a, yarda da kulawar jama’a, karfafa karfin wakilai, da kuma ƙoƙarin yi wa jama’a hidima.
Na shida shi ne inganta dandalin bayyana ra’ayoyin jama’a na dimokuradiyya na majalisar wakilan jama’ar kasar, da inganta tsarin aiki na karbar ra’ayin jama’a da hada hikimar jama’a. Na bakwai shi ne karfafa wayar da kan jama’a game da harkokin siyasa, da kokarin gina wata tawaga ta ‘yan majalisar jama’a masu tsayin daka a siyasance, masu yi wa jama’a hidima, mutunta doka, da kuma inganta dimokuradiyya, ta yadda za a bayar da sababbin gudunmawa ga ci gaban dimokuradiyyar jama’a a kan bunkasa tsarin dimokuraddiyar jama’a a dukkan matakai da kuma tabbatar da cewa jama’a su ne masu mulkin kasar.
A shekarar 2022, an yi nasarar gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, inda aka zana wani babban tsari na gina kasa mai bin tsarin gurguzu ta zamani bisa daga dukkan fannoni, da kuma sa kaimi ga babban farfagandar al’ummar kasar Sin tare da zamanantar da kasar Sin. A cikin sabuwar shekara, tarukan kasa guda biyu za su sake yin wata sabuwar tafiya, da yada ra’ayoyin jama’a, da tattara ra’ayoyinsu, da tattara karfinsu, da kuma ci gaba da busa kiraye-kirayen zamani na sabuwar tafiya. (Safiyah Ma)