Babban bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana ce bai bayar da wani sabon umarni ga bankunan kasuwanci ba kan hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar Juma’ar da ta gabata na bayar da umarnin a rika amfani da tsofaffin takardun naira tare da sabbi har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.
Kwamitin alkalai na mutane bakwai karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro, ya bayyana lamarin a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa, umarnin da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bai wa CBN na sake sauya fasalin naira tare da cire tsofaffin takardun kudi na naira 200, 500 da 1,000, ba tare da tuntubar jihohi ba, majalisar zartarwa ta kasa, majalisar jihohi da sauran masu ruwa da tsaki.
Daily Trust ta ruwaito cewa an samu rudani a tsakanin bankunan kasuwanci da ‘yan kasuwa biyo bayan rashin bayar da umarnin da CBN bai yi ba na karbar tsofaffin takardun kudi na naira 500 da 1000. Kakakin babban bankin na CBN, Isa Abdulmumin ya bayyana cewa CBN bai fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan wannan batu.
Sai dai wani babban jami’in bankin da ya zanta da Daily Trust ya ce: “Tsoho da kuma sababbin takardun kudi duk doka ta amince da su, kuma a halin yanzu bankuna suna ba da su ga kwastomomi. Ka da ‘yan Nijeriya su yi watsi da kudi ko tsoho ko sabo.”
Akwai karin bankunan kasuwanci a fadin kasar nan za su fara raba tsofaffin takardun kudi na naira 500 da 1000 ga kwastomominsu.
Hakan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da Bankin GTB ya fara raba tsofaffin takardun kudi a rassansa a fadin kasar a ranar Litinin.
Binciken da wakilinmu ya yi a Legas ya nuna cewa bankuna sun fara bayar da tsofaffin takardun kudi na naira ga kwastomomi a na’urar ATM daban-daban da kuma kan kantuna.
Reshen bankin Zenith da ke garin Festac ya biya tsofaffin takardun kudi ga abokan ciniki a kan kantuna. Haka kuma na’urorin ATM da ke rassan bankin UBA a kusa da gadar Agege-Pen Cinema da GTB da ke unguwar Ikeja a Legas, su ma suna raba tsofaffin takardun kudi.
Binciken ya kuma nuna cewa bankin WEMA ya umurci rassansa da su fara raba tsofaffin takardun kudi na naira 500 da 1000 a fadin kasar nan.
Har ila yau, wani jami’in bankin Zenith wanda ya so a sakaya sunansa ya ce reshen da suke sun sami umarnin fara raba tsofaffin takardun kudi ga abokan cinikinmu. Wani ma’aikacin bankin Zenith, Barista Dike Amadi ya ce, “An biya ni tsohuwar kudi na naira 500 a yammacin yau a wani reshen bankin Zenith da ke Fatakwal.”
Haka shi ma wani abokin ciniki mai suna Aina Dipo, ya ce, “Yanzu ana bayar da tsofaffin takardun kudi na naira 500 da 1000 a Osogbo, Jihar Osun.”
Bincike da aka yi a bankin First Bank da Polaris da kuma bankin Unity, ya nuna cewa tsohon naira 200 ne kawai suke rabawa kamar yadda CBN ya umarta.
Wani manajan bankin First Bank da ke Kano ya ce, “Ba mu samu wani daftari daga CBN ba na karbar tsofaffin takardun kudi, kuma shi ya sa hakan bai gudana ba kamar yadda muke magana a halin yanzu.”
‘Yan Kasuwa Suna Kin Amsar Tsafaffin Kudi
Sai dai kuma an sake samun wani sabon salo a rikicin, inda manyan kantuna da gidajen mai da direbobin bas na ‘yan kasuwa a wasu sassan Legas ke kin amincewa da tsofaffin takardun kudi.
Olaiya Simileoluwa, wani mazaunin Legas ya ce, “Akwai rudani a cikin wannan lamari. Kotun koli ta ce tsofaffin takardun naira za su ci gaba da aiki har zuwa watan Disamba, bankuna sun fara rarraba tsofaffin takardun kudi, amma kuma direbobin bas, manyan kantuna, gidajen mai, da sauran su ba sa karbar tsofaffin kudin. An dai jefa kasar nan cikin babban rudani. ”
Hakazalika, Kate Hensley Haziel wadda ita ma da ke zaune a Legas ta ce, “Ina ganin bayan hukuncin kotun koli, tsofaffin naira 500 da 1000 za su ci gaba da zama kudi bisa tsarin doka har zuwa Disamba 2023. Akwai bukatar CBN ya yi magana da ‘yan Nijeriya. Mutane da yawa har yanzu suna cikin rudani game da ko za su karbi tsoffin kudin ko kuma a’a. ”
‘Shugaba Buhari Ya Bukaci CBN Ya Martaba Hukuncin Kotun Koli’
Wani masani kan harkokin kudi, Gbolade Idakolo, ya ce ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci gwamnan CBN da martaba hukuncin kotun koli.
“Tsarin sake fasalin naira ya durkusar da tattalin arzikin kasa da sama da tiriliyan guda a cikin harkokin kasuwanci. Yawancin kananan masana’antu sun rufe shagunansu saboda mu’amalarsu da tsabar kudi kai-tsaye.
“Tsarin ya kara wahalhalu ga al’ummar da ke cikin damuwa, kuma hukuncin kotun koli zai kasance babban taimako ne ga mutanen kasar nan,” in ji shi.