Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, Peter Obi, ya zargi gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da kin taimaka masa.
Obi wanda ya zanta da gidan talabijin na Arise a ranar Litinin, ya kuma yi zargin an tafka magudi a sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a Ribas, inda ya bayyana cewa ya yi nasara a jihar.
- Yankin Daji A Kasar Sin Ya Karu Da Kadada Miliyan 22 Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata
- Da Dumi-Dumi: CBN Ya Amince Da Ci Gaba Da Amfani Da Tsofaffin Takardun Naira
A Ribas, Bola Tinubu na jam’iyyar APC, ya samu nasara da kuri’u 231,591 yayin da LP ta samu kuri’u 175,071.
Obi ya ce mutane sun zabe shi ba tare da la’akari da kabilanci ba, amma bisa ga asalinsa, ya kara da cewa ya ma samu kuri’u daga ‘yan asalin Legas fiye da na bakin haure.
“A yankin Kudu-maso-Gabas ma haka lamarin yake, mutane sun san ni, mutane sun san abin da na tsayawa a kai, mutane sun san na cika alkawuran da na dauka. Mutane sun san cewa na kiyaye abin da na fada.”
A halin da ake ciki kuma, a kwanan baya Wike ya ce Obi ne gwarzon zabe, yana mai cewa mulki zai ci gaba da wanzuwa a Arewa idan shi (Obi) bai tsaya takara ba.
Wike, wanda ya yi jawabi ga ‘yan kasuwar kabilar Inyamurai a wani dakin taro na garin Fatakwal a ranar Asabar din da ta gabata, ya ce kasancewar Obi a zaben ya tabbatar da fitowar dan kudu a matsayin zababben shugaban kasa.
A cewar gwamnan, jihohin da Obi ya samu nasarar da jam’iyyar PDP ta samu kuma ta bai wa Arewa damar ci gaba da rike madafun iko ta hannun dan takarar PDP, Atiku Abubakar.